Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa aka ga Buhari ba takunkumi a fuskarsa a Daura

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa aka ga Buhari ba takunkumi a fuskarsa a Daura

- An hangi shugaban kasa yana zantawa da wasu gwamnoni ba tare da sanya takunkumi ba

- A satin da ya gabata ne dai shugaban ya rattaba hannu kan dokar da ta tilasta amfani da takunkumin fuska

- Fadar shugaban kasa ta ce shugaban ya sanya takunkumi kuma bai cire ba har sai da aka gama taron

A baya bayan nan ne shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a dokar kariya daga cutar coronavirus da ke tilasta amfani da takunkumin fuska, SaharaReporters ta ruwaito.

Dokar ta tanadi tara ko daurin wata shida ko gaba daya biyun ga duk wanda ya karya dokar.

Amma a karshen mako, an ga shugaban kasar yana tattaunawa da wasu gwamnonin APC a wajen sabunta rajistar sa ta jam'iyyar APC a Daura ba tare da sanya tukunkumin ba.

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da aka ga Buhari ba takunkumi a fuskarsa a Daura
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da aka ga Buhari ba takunkumi a fuskarsa a Daura. Hoto: Sahara Reporters
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa amarya rasuwa kwanaki 5 bayan an daura aurenta a Kano

Shugaban kasar ya karya ka'idar da kwamitin yaki da cutar corona na fadar shugaban kasa ya sanya, cewa yan Najeriya su rufe hanci da baki yayin da suke zantawa da mutane don kare su daga dauka ko yada cutar.

Jam'iyyar adawa, PDP, da wasu yan kasa a kafafen sada zumunta sun soki yadda shugaban ya karya dokar da ya rattaba hannu da kan shi, wanda ya maida amfani da takunkumin fuska wajibi a wuraren gwamnati, daga cikin matakan kariya daga COVID-19.

Da yake bayani ranar Litinin, mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya ce shugaban ya sanya takunkumin kuma bai cire ba sai da zai yi magana a amsa kuwwa.

KU KARANTA: Dan majalisar APC ya bindige ɗan fashi da makami har lahira a Sokoto

Da yake zantawa da gidan talabijin na Channels, Shehu ya ce, "mutane ba su fahimci abin ba. Shugaban kasa na sanya da takunkumin fuska har aka gama taron. Ya cire ne lokacin da zai bayani a amsa kuwwa. Kawai wasan kwaikwayo ne irin na PDP."

An kuma soki yadda gwamnoni 10 suka yi wa shugaban rakiya duk da dokar bada tazara da hukumomin lafiya suka sanya.

Mai magana da yawun shugaban kasar, ya ce babu komai game da adadin gwamnoni ko jagororin APC a tawagar.

"Wannan an yi ne don janyo hankali wajen sabunta rajistar. Dole mu nuna yan kasa muna goyon baya kuma ko wane dan jam'iyya yana ciki.

"Suka ce irin ta jam'iyyu marasa tsari da baza su iya shirya irin wannan ba, muna tausaya mu su," inji Shehu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel