Dakarun soji sun sheke 'yan bindiga 2 a Kagarko har lahira

Dakarun soji sun sheke 'yan bindiga 2 a Kagarko har lahira

- Sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Thunder Strike sun halaka 'yan bindiga biyu a Kagarko

- Sojojn sun kai samame ne bayan samun rahotanni da suka yi a kan titin Sabon Iche-Kagarko da ke Kaduna

- A take suka kashe 2 yayin da sauran suka tsere da miyagun raunikan da suka samu daga harbin bindiga

Dakarun soji karkashin rundunar Operation Thunder Strike a daren Litinin sun halaka 'yan bindiga biyu a kan titin Sabon Iche-Kagarko a karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan bindigan suna daga cikin miyagun da suka addabi yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Hakazalika, rahotannin tsaro daga jihar Kaduna sun tabbatar da cewa dakarun sun yi lambo a kan hanyar bayan bayanan sirri da aka sanar musu na kaiwa da kawowar 'yan bindiga a yankin.

KU KARANTA: Hotuna: Ana saura kwana 3 daurin aure, uwargida ta kashe budurwar mijinta a Kano

Dakarun soji sun sheke 'yan bindiga 2 a Kagarko har lahira
Dakarun soji sun sheke 'yan bindiga 2 a Kagarko har lahira. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

A wata takarda da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ya saka hannu, ya ce 'yan bindigan sun shiga yankin kuma sojin sun ragargajesu.

Ya ce dakarun sun samu nasarar kashe biyu daga cikin 'yan bindigan kuma sun kwashe gawawwakinsu yayin da sauran suka tsere da raunikan harbi.

Ya yi kira ga mazauna yankin da su kai rahoton duk wanda suka ga yana neman taimakon masana kiwon lafiya daga raunikan bindiga.

Aruwan ya ce: "Mazauna yankin su tabbatar da cewa duk wanda aka kama yana baiwa 'yan bindiga taimako na daga fannin lafiya za a kama shi a matsayin dan bindiga."

KU KARANTA: Bidiyon yaro yana kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba ya nishadantar

A wani labari na daban, wani dan sanda mai mukamin sifeta ya rasu inda wasu suka raunata bayan harin da 'yan bindiga suka kai jihar Ribas, Channels Tv ta wallafa.

Hukumar 'yan sandan jihar Ribas ta ce kusan 'yan bindiga 17 ne suka kai gagagrumin hari kan jami'an 'yan sandan da aka tura Borikiri a Fatakwal a daren Lahadi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni a wata takarda da ya fitar, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Joseph Mukan ya bada umarnin zakulo wadanda suka aikata wannan laifin da gaggawa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel