Bidiyon yaro yana kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba ya nishadantar
- Wani karamin yaro ya nuna wa mahaifiyarsa cewa baya son barinta yayin da yake bayyana mata irin soyayyar da yake mata
- A bidiyon da ya bazu a kafar sada zumunta, an ga karamin yaron yana rangada kuka bayan mahaifiyarsa ta ce ba za ta aure shi ba
- A yayin da yaron ke bayyana irin soyayyar da yake wa mahaifiyarsa, ya ce baya son barinta har abada
Wani bidiyon karamin yaro ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani inda yake rangadawa mahaifiyarsa kuka saboda ta ce ba za ta iya auren shi ba.
A bidiyon, an ga yaron karami yana sanar da mahaifiyarsa irin son da yake mata kuma ya fi son ta a kan kowa a fadin duniya.
Yayin martani, mahaifiyarsa ta ce tana matukar son shi itama amma ba za ta iya auren shi ba. Ta kara da kokarin yi mishi bayanin yadda aure yake amma ya kasa fahimta.
KU KARANTA: An harbe mutum 1 bayan mutanen Kafanchan sun fito zanga-zanga kan karin kudin lantarki
A take ta yanke shawarar kai shi wurin mahaifiyarta, wato kakarshi domin ta ganar da shi yadda aure yake.
KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: APC ta lashe dukkan kujeru 44 na jihar Kano
Babu jimawa da wallafa wannan bidiyon jama'a suka fara tsokaci a kai.
Wata mai amafani da suna @merryalyce_m ta rubuta: "Zuciyata ta karaya da wannan kyakywan yaro."
@rachel_rainbow02 kuwa cewa tayi: "Da na shima haka yake yi. Yana cewa baban shi, da ni da shi duk ma'aurata ne. Yana kuka mai tsanani idan nace dole sai ya nemi wata ya aura idan ya girma. Yana cewa ba zai taba barina ba."
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum a ranar Lahadi ya gabatar da motocin alfarma biyu ga sabon Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Elkanemi domin saukaka masa tafiye-tafiye da al'amuran mulkinsa.
Daya daga cikin motocin akwai kirar SUV Lexus ta 2020 sai wata kirar Toyota Hilux ta 2020.
Babban sakatare a ma'aikatar kananan hukumomi da masarautu, Tarfaya Asariya, wanda ya samu rakiyar kwamishinan ayyukan noma, Injiniya Bukar Talba ne suka mika motocin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng