'Yan bindiga sun halaka sifetan 'yan sanda, sun raunata wasu a jihar Ribas
- 'Yan bindiga sun halaka wani dan sanda mai mukamin sifeta a jihar Ribas yayin da suka raunata wasu
- 'Yan bindiga 17 sun kai wa 'yan sanda da ke yankin Borikiri a Fatakwal mummunan hari a daren Lahadi
- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya bukaci a gaggauta zakulo miyagun da suka yi wannan aika-aikar
Wani dan sanda mai mukamin sifeta ya rasu inda wasu suka raunata bayan harin da 'yan bindiga suka kai jihar Ribas, Channels Tv ta wallafa.
Hukumar 'yan sandan jihar Ribas ta ce kusan 'yan bindiga 17 ne suka kai gagagrumin hari kan jami'an 'yan sandan da aka tura Borikiri a Fatakwal a daren Lahadi.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, SP Nnamdi Omoni a wata takarda da ya fitar, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Joseph Mukan ya bada umarnin zakulo wadanda suka aikata wannan laifin da gaggawa.
KU KARANTA: Zaben kananan hukumomi: APC ta lashe dukkan kujeru 44 na jihar Kano
Ya kara da bayyana cewa tuni aka dauke gawar sifetan kuma aka adana ta a ma'adanar gawawwaki.
Harin da aka kai wa 'yan sandan an yi shi ne kasa da sa'o'i 24 bayan cafke wani sajan din 'yan sanda mai suna Ibrahim Odege da wani farar hula, Sampson Inomoghe a Fatakwal yayin da suke fashi da makami.
KU KARANTA: 2023: Wallafa hoton El-Rufai da Tinubu ya janyo wa Bashir El-Rufai mugun zagi daga jama'a
A wani labari na daban, sojoji biyar da suka hada da hafsin soja daya daga bataliya ta 117, 28 Task Force Brigade ne suka rasu yayin da wasu 15 suka jigata bayan sun fadawa wani bam da mayakan Boko haram suka dasa a wani kauye da ke kudancin jihar Borno a ranar Alhamis, majiyoyi suka tabbatar.
An gano cewa lamarin ya faru wurin karfe 10:20 na safe kusa da kauyen Kwada Kwamtah Yahi da ke karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.
Motar sojin Najeriyan ta bi ta kan wani gagarumin bam da mayakan ta'addancin suka dasa, ya kashe wani babban soja tare da wasu kanana hudu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng