Jika Wahal Da Kaka: Bidiyon Wasu Tagwaye Da ke Kwaikwayon Tafiyar Kakansu Ya Ja Hankali

Jika Wahal Da Kaka: Bidiyon Wasu Tagwaye Da ke Kwaikwayon Tafiyar Kakansu Ya Ja Hankali

  • Bidiyon wasu kananan yara biyu da ke kwaikwayon yadda kakansu ke tafiya a lankwashe saboda tsufa ya yadu a soshiyal midiya
  • A bidiyon, an gano yaran wadanda tagwaye ne suna biye da kakansu a baya sannan suna tafiya tamkar shi cike da shakiyanci
  • Shafin 4sunshine Baby ne ya wallafa bidiyon a TikTok kuma ya samu mutum fiye da miliyan 13 da suka kalla

Bidiyon wasu kananan yara biyu suna kwaikwayon yanayin tafiyan kakansu ya samu mutum fiye da miliyan 13 da suka kalla a dandalin TikTok.

Shafin 4sunshine Baby ne ya wallafa bidiyon inda ya ce an bar yaran ne tare da kakansu a kwanan nan.

Jikoki da kakansu
Jika Wahal Da Kaka: Bidiyon Wasu Tagwaye Da ke Kwaikwayon Tafiyar Kakansu Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@4sunshinebaby
Asali: UGC

A dan gajeren bidiyon wanda tsawonsa bai wuce sakan 8 ba, an gano yaran biyu suna bin kakan nasu a baya.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Ke Samun N20,000 Kullun Daga Siyar Da Alale, Yana Shiga Kamar Ma’aikacin Banki

Bidiyon tagwayen yara suna tafiya tamkar kakansu

Dattijon na tafiya ne a lankwashe saboda tsufa, don haka sai yaran suka dungi kwaikwayonsa a baya sannan suna tafiya tamkar shi harda sanya hannunsu a baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shakka babu, sun yi nasarar kwaikwayonsa daidai inda suka dunga debe masa kewa yayin da suke motsa jiki.

Mutanen da suka ci karo da bidiyon sun bayyana shi a matsayin mai ban dariya da sha'awa.

Bidiyon na dauke da taken:

"Wadannan kananan gayun sun kasance tare da kakansu a kwanan nan, sannan a yau sun koma kamar shi."

A yanzu haka, bidiyon ya samu 'likes' 261k da martani fiye da 3000.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Princess Belle ta ce:

"Hakan ya yi kyau. Na so ace yarana sun samu damar ganin kakansu amma mutuwa ta dauke mahaifina - abokina da wuri."

Kara karanta wannan

Bidiyon Shugaban Kasan South Sudan Yana Fitsari A Wando Ana Tsakiyar Taro

@yarima538 ya yi martani:

"Yara da kakansu abokai ne."

@user4045928819887 ya ce:

"Na karshen shine ainahin kakan."

@user5010847000714 ya yi martani:

"Lokacinsu na nan zuwa."

@Erdal. ya yi martani:

"Yaro na biyun ya fi iyawa."

@Casilda Lepre ta ce:

"Na so haka. Kanan yaran akwai ban dariya."

@Chengg lee ya ce:

"Kada ku yi gaggawa duk za ku kai wajen."

A wani labarin kuma, wani matashi dan Najeriya ya maka budurwarsa a kotu bayan ta zagi matarsa a soshiyal midiya.

Kotu ta mallaka masa tsabar kudi naira miliyan takwas da ta ci tarar budurwar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng