Zanga-zanga ya barke a Fatakwal bayan dan sanda ya bindige direban Keke-Napep kan N100 (Bidiyo)

Zanga-zanga ya barke a Fatakwal bayan dan sanda ya bindige direban Keke-Napep kan N100 (Bidiyo)

- Duk da zanga-zangar EndSARS, wani dan sanda ya kuma kashe wani ba gaira ba dalili

- Rikici ya kaure a birnin Fatakwal ranar Alhamis sakamakon wannan kisa

- Abokan aikin direban sun dauki gawarsa kan titi suna zanga-zanga

Rikici ya barke a unguwar Rokpoku na birnin Fatakwal sakamakon bindige direban a-daidaita-sahu (Keke Napep).

Wannan abu da ya faru misalin karfe 7 na safiya Alhamis, a hanyar tashar jirgin sama ya haddasa rikici a yankin.

Wasu fusatattun matasa da abokan direban sun toshe hanyar suna zanga-zanga.

Wani mai idon shaida ya ce dan sandan ya kashe direban ne saboda ya ki bashi na goron N100 da ya bukata.

The Cable ta ce kakakin hukumar yan sandan jihar, Nnamdi Omooni, ya tabbatar da hakan nda yace an damke jami'in da yayi kisan.

"Ina sane da abinda ya faru a Rukpokwu. Daya daga cikin jami'anmu ya kashe wani matukin keke da safen nan. An kwace makamin dan sandan kuma an tsareshi yanzu," yace.

"Mun tura mazajenmu wajen domin kwantar da kuran da kuma hana barkewar rikici."

"Muna kira ga mutane sun kwantar da hankulansu, su bari mu hukuntashi."

"Kisan dans anda ko kona ofishin yan sanda ba zai dawo da wanda aka kashe ba; inamma hakan munanan abu zai yi."

Wannan na zuwa watanni biyu bayan zanga-zangar EndSARS ta barke a Najeriya.

KU DUBA: Akwa Ibom: An auka ofishin CPS, an sace wasu tulin kudi a gidan Gwamnati

Zanga-zanga ya barke a Fatakwal bayan dan sanda ya bindige direban Keke-Napep kan N100 (Bidiyo)
Zanga-zanga ya barke a Fatakwal bayan dan sanda ya bindige direban Keke-Napep kan N100 (Bidiyo) Hoto: premiumtimes.com
Asali: UGC

Kalli bidiyon:

KU DUBA: Lawan: 'Yan majalisar dattawa ba kansu suke wa aiki ba, Ahmad Lawan

A bangare guda, kungiyar dattawan Arewa a ranar Talata ta alanta cewa ba za ta sake lamuntan harin da ake kaiwa mutan Arewa dake zama a kudancin Najeriya ba.

Shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdulahi ya bayyana hakan a garin Fatakwal inda suka gana da al'ummar Arewa dake zama a jihar Rivers, rahoton Punch.

Yayinda ya bayyana cewa sun zo jihar domin jajantawa 'yan uwansu da aka kai wa hare-hare yayin zanga-zangar EndSARS, ya ce abin ya bayyana karara wasu yan yankin Inyamurai (kudu maso gabas) ke kashe yan Arewa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng