Buhari ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu

Buhari ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu

- Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin bude wasu iyakokin kan tudu guda hudu

- Ministar Kudi ce ta sanar da hakan yayin tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron FEC

Labari da dumi-duminsa da Legit.ng Hausa ta samu daga shafin gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayar da umarnin bude iyakokin kan tudu guda hudu.

A cikin takaitaccen kanun labarai da Channels ta wallafa, ta bayyana cewa umarnin bude iyakokin zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamba, 2020.

Iyakokin guda hudu da za'a bude sune kamar haka: Illela a Jihar Sokoto, Maigatari a jihar Jigawa, dukkansu a arewacin Nigeria.

Sai kuma iyakar Seme da ke Jihar Legas, yankin kudu maso yamma, da iyakar Mfun da ke yankin kudu maso kudu.

KARANTA: Umarnin rufe layukan waya: Yadda za'a duba matsayin lambar NIN daga wayarku ta hannu

Daily Nigerian ta rawaito cewa ministar kudi, Zainab Ahmed, ce ta sanar da hakan ranar Laraba yayin ganawarta da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC).

Buhari ya bayar da umarnin bude iyayakon kan tudu guda hudu
Buhari ya bayar da umarnin bude iyayakon kan tudu guda hudu @Channels
Asali: Twitter

Sanarwar bude iyakokin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar NSMC ta kwatanta rashin tsaron Najeriya da rashin tsaron iyakoki, inda ta bayyana cewa hakan ne dalilin da yasa aka gaza cin nasara akan 'yaki da 'yan bindiga da Boko Haram.

KARANTA: Masari ne ya kamata ya shige gaba, ya jagoranci tawagar rundunar ceton daliban Kankara; in ji kawararre a fannin tsaro

Ta ce matsawar gwamnatin tarayya tana son cin nasara a kan rashin tsaro ta wuraren tafkin Chadi, wajibi ne a kula kwarai, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Wadannan kadan ne daga cikin hanyoyin da za a tsare 'yan Najeriya daga cutarwar 'yan bindiga, kamar yadda mambobin kwamitin suka tattauna don samar da tsaro a kasar nan.

A ranar Talata ne Legit.ng Hausa ta rawaito cewa Sanatoci sun koka akan gazawar shugaba Buhari wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da Najeriya ke fama da ita, kmar yadda Punch ta rawaito.

Sun kuma tunawa Shugaban ƙasar irin ƙarfin ikon da doka ta basu na tsige Shugaban ƙasa kamar yadda yake a kundin dokokin Najeriya.

Sanatoci sun yi niyyar ɗaukar ƙwararan matakai da suka haɗar da dakatar da kasafin kuɗin 2021, wanda hakan zai tilastawa shugaban ƙasa aiwatar da ƙudirinsu da gaske.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel