Hotuna tare da bayani a kan fitaccen bangon Benin mai kama da bangon duniya na China

Hotuna tare da bayani a kan fitaccen bangon Benin mai kama da bangon duniya na China

- Bangon Benin mai cikakken tarihi ya kasance wata babbar alama da ke nuna cewa 'yan Afrika suna da wayewa tun kafin zuwan turawa

- An cire ginin babban bangon ne a 1897 wanda Turawa suka dauka nauyi, lamarin da yasa wani babban tarihin yaniin ya goge

- Amma kuma, akwai wurare masu yawa a masarautar Benin kamar gidan Obasagbon wadanda ke da irin wannan bangon

Wani babban tarihi na nahiyar Afrika da ba a iya mayewa da shi yana masarautar Benin, gari mai matukar tarihi kuma har yanzu yana daukar hankali.

An gano cewa an barar da bangon babbar masarautar a 1897, lamarin da ya matukar girgiza babban tarihin Benin da kuma goge tarihin wayewar 'yan nahiyar tun kafin zuwan Turawa.

Ya fi tsawon bangon China wanda ake ikirarin shine bangon duniya

Fiye da karni hudu da suka gabata, bangon Benin yana bai wa jama'ar Edo kariya tare da wayewarsu.

Kamar yadda masanin kimiyya Fred Pearce yace, bangon Benin yafi bangon China tsayi sau hudu.

Ya shiga cikin littafin Guinness

Fred ya kara da cewa, littafin Guinness na duniya na 1974 ya kwatanta bangon Benin da aiki tukuru da wani dan Adam ya taba a wancan zamanin.

Daga bisani ya zo babu shi, Turawa sun rushe shi

Rashin wannan bango mai cike da tarihi ya faru ne a karni na 15, lamarin da ya kawo rikici akan iyakoki a 1980s

KU KARANTA: Da duminsa: Shugaban INEC ya sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023

Hotuna tare da bayani a kan fitaccen bangon Benin mai kama da bangon duniya na China
Hotuna tare da bayani a kan fitaccen bangon Benin mai kama da bangon duniya na China. Hoto daga en.wikipedia.org
Asali: UGC

KU KARANTA: Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama

A wani labari na daban, MSN Money kungiya ce da ke kula da hada-hadar kudi, hannayen jari, kadarori da kuma lamuni a duniya.

Ta yi bincike a kan gini 30 mafi tsada da darajar kudi a fadin duniya kuma kasar Saudiya ce a kan gaba da gine-gine biyu. Ga dai jerin gini 10 mafi darajar kudi a duniya tare da hotunansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel