Kyakyawar budurwa ta sha kunya, ta ce tana son saurayi amma yace ta cigaba da nema

Kyakyawar budurwa ta sha kunya, ta ce tana son saurayi amma yace ta cigaba da nema

- Budurwa mai karancin shekaru ta sha kunya a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter

- A yayin da wani saurayi ya wallafa hotonsa, ta nemi shigar da kanta a wurinsa

- Amma sai dai saurayin ya gwasaleta inda ya bukaci da ta cigaba da nema ko za ta samu

Wata budurwa mai karancin shekaru ta mika wa wani saurayi soyayyar ta, sai dai hakon nata bai cimma ruwa ba.

Wata budurwa 'yar Najeriya tayi amfani da shafin sada zumuntar zamani ta Twitter inda take amfani da suna @lil_keffi, ta nuna wa wani santalelen saurayi ra'ayinta.

Ya gwada wa budurwar shi dai bashi da ra'ayi a kanta, sai dai ta kara gaba, watakil ta samu wani saurayin da zata burge amma ba shi ba.

Al'amarin ya fara ne, a lokacin da wani santalelen Injiniya mai suna Anietie Akpanumoh ya bayyanar da hotonsa mai burgewa.

Budurwar mai suna @lil_keffi, ta daure kuma ta dage ta kafar sada zumuntar ta bayyanar masa da sakon zuciyar ta.

Saurayin yayi murmushi mai kayatarwa a hoton da yasa har yace, "wannan murmushin bai kai ciki ba, ina bukatar hutun mako guda."

@lil_keffi batayi kasa a guiwa ba bayan ta ga hoton, sai ta tambayeshi inda ta ce, "ina fatan wannan zoben dake hannunka ba na aurenka bane?".Ashe tarkon ta bazai kama kurciya ba.

KU KARANTA: Za mu gina sabuwar Najeriya: Lai Mohammed ya yi bayanin shagalin cikar Najeriya shekaru 60

Saurayin ya amsa mata da, "Eh bana aure na bane". Sai budurwar ta cigaba da tambayar sa, ganin ya bata amsa: "Shin kana bukatar wadda zata dinga nuna maka kulawa, wadda zata dinga tambayarka yadda ka tashi, da yadda zaka kwanta? Ko kuma in nema a gaba?"

Akpanumohan ya amsa wa budurwar da, "eh, gaskiya sai dai ki nema a gaba."

Wannan maganar tasu ta kawo cece-kuce a kafar sada zumuntar. Inda mutane da dama sukayi ta maganganu kala kala, har wasu suna ganin cewa saurayin ya wulakanta budurwar, wasu kuma na ganin bai dace mace ta zubar da ajinta haka ba.

Kyakyawar budurwa ta sha kunya, ta ce tana son saurayi amma yace ta cigaba da nema
Kyakyawar budurwa ta sha kunya, ta ce tana son saurayi amma yace ta cigaba da nema. Hoto daga @lil_keffi/Twitter
Source: Twitter

KU KARANTA: An bayyana hamshakin mai kudi dan Najeriya a cikin mutane 100 da suka fi kowa alfarma a duniya

A wani labari na daban, wata mata mai dauke da juna biyu ta fada cikin ruwa don ceton rayuwar mijinta lokacin da wani katon kifi ya kai mishi farmaki a Florida.

A ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba wani kifi ya kaiwa wani mutumi mai suan Andrew Eddy, mai shekaru 30 da haihuwa farmaki, yayin da yake cikin jirgin ruwansa a yankin Sombrero a Florida.

A yadda rahotonni suka nuna, katon kifin ya ciji kafadar mutumin ne, sakamakon haka ya sanya take a wajen jirgin ya kife cikin ruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel