Juyin mulki: ECOWAS ta dakatar da Mali, za ta yanke mata hukunci mai tsauri

Juyin mulki: ECOWAS ta dakatar da Mali, za ta yanke mata hukunci mai tsauri

A ranar Talata, kungiyar hadin kan kasashen Afrika na yamma, sun kushe abinda ya faru a kasar Mali tare da daukar alkawarin ladabtarwa wanda ya hada da tara.

Sojojin adawa sun kama shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita da firayim minista Boubou Cisse a ranar Talata, bayan makonni da aka kwashe ana rikicin siyasa a kasar.

Lamarin ya ci gaba inda sojojin suka kwace babban barikin sojin da ke babban birnin Bamako da safiyar ranar.

A wata takarda da ECOWAS ta aike musu, ta ce dukkan kasashen Afrika ta yamma za su rufe iyakokin da ke tsakaninsu da Mali na kasa da na sama kuma za ta ci tararsu.

Kungiyar kasashen 15 wanda ya hada da Mali, ta kara da cewa za ta dakatar da kasar daga cikin masu yanke hukuncinta.

"ECOWAS cike da jimami ta gano yadda sojin kasar Mali suka kwace mulki," takardar ta ce, wacce aka wallafa da harshen Faransanci.

Juyin mulki: ECOWAS ta dakatar da Mali, za ta yanke mata hukunci mai tsauri
Juyin mulki: ECOWAS ta dakatar da Mali, za ta yanke mata hukunci mai tsauri. Hoto daga Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yaki da rashawa: 'Yan Najeriya sun caccaki Ganduje a kan tsokacinsa

Mali ta kasance tsundum cikin rikicin siyasa tun a watan Yuni inda aka dinga bukatar Shugaban kasa Keita ya yi murabus.

A ranar 5 ga watan Yuni ne 'yan adawar suka fito domin zanga-zanga tare da nuna fushinsu a kan lalacewar tattalin arzikin, rashawa a gwamnati da kuma ta'addanci.

Kungiyar adawar ta ci gaba da zanga-zanga inda a watan jiya har rayukan mutane 11 suka salwanta a cikin kwanaki uku bayan rikicin da ya barke.

A kokarin dakile rikicin, ECOWAS ta shiga lamarin domin yin sasanci.

Kungiyar ta yanke shawarar hada gwamnatin hadin kai da sauran matakai a watan da ya gabata, amma Keita ya soki hakan.

Zanga-zangar ranar 5 ga watan Yuni ta ci gaba da tada hankali tare da assasa cewa sai Keita ya sauka daga mulkin kasar.

A ranar Litinin, 'yan adawar sun fitar da sabon salon yakar gwamnatin kasar. Sojoji 'yan adawa sun damke Keita mai shekaru 75 a wajen babban birnin kasar.

Amma kuma, shugaban kasar Mali a ranar Laraba ya ce ya yi murabus domin hana "zubar da jini", awanni bayan da rundunar soji suka yi caraf da shi, a yunkurin juyin mulki. Cafke shugaban kasar da yunkurin juyin mulkin, yana zuwa ne bayan shafe sama da watanni ana rikicin siyasa a kasar Mali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng