Yanzu-yanzu: IGP ya yi magana a kan bukatar bada belin Magu

Yanzu-yanzu: IGP ya yi magana a kan bukatar bada belin Magu

Sifeta Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bukacin Tosin Ojaomo, lauyan dakataccen shugaban hukumar yaki da rashawa, Ibrahim Magu, da ya mika bukatar belin wanda yake karewa gaban kwamitin da ke bincikarsa na fadar shugaban kasa.

Sifeta janar na 'yan sandan ya tabbatar da cewa ba 'yan sanda bane ke bincikar Magu, hakazalika ba su bane ke garkame da shi. Kwamitin bincike na fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ke da iko da shi.

Adamu ya sanar da hakan ne a wata wasika mai kwanan wata 14 ga Yulin 2020, wacce ta zama martani ga bukatar belin da lauyan Magu, Tosin Ojaomo, ya mika garesa.

A wasikar, lauyan dakataccen shugaban EFCC ya bukaci a bada belin wanda yake karewa saboda an tsaresa tun daga ranar 6 ga watan Yulin 2020.

Kamar yadda wasikar tace: "Duba da wasikarku mai lamba da kwanan wata OOC/TOL/89A/07/2020, 10 ga watan Yuli.

"Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya na umartarku da ku janye cewa da kuke 'yan sanda ke bincikar CP Ibrahim Magu, wato wanda kuke karewa.

"Ba hukumar 'yan sanda ke tsare da shi ba illa iyaka kwamitin bincike na fadar shugaban kasa ne ke bincikar ayyuka hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa.

“A don haka, Sifeta Janar na 'yan sandan na shawartarku da ku mika bukatar belinku ga shugaban kwamitin binciken na fadar shugaban kasa."

Yanzu-yanzu: IGP ya yi magana a kan bukatar bada belin Magu
Yanzu-yanzu: IGP ya yi magana a kan bukatar bada belin Magu. Hoto daga The Punch
Asali: UGC

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Sabbin mutum 463 sun sake harbuwa da korona a Najeriya

A wani labari na daban, wani rahoton jaridar Vanguard ya bayyana cewa, dakataccen shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, zai fara yajin cin abinci.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, Magu ya yanke wannan hukuncin ne bayan ganowa da yayi cewa fadar shugaban kasa za ta iya tsareshi har sai ya amsa laifukan da ake zargin sa da su.

Magu na fuskantar kwamitin fadar shugaban kasa na bincike bayan Antoni janar din tarayya, Abubakar Malami, ya bankado cewa ana sake kwashe kudin kasar nan da ake samowa.

Tuni, wasu 'yan siyasa da masu hannu da shuni a Najeriya da kasashen ketare, masu ikirarin cewa Magu da wasu jami'an EFCC sun damfaresu, suka fara mika kokensu a kan yadda aka kwace musu kudadensu ko kadarorinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel