Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta

Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta

Daya daga cikin wadanda suka ga yadda 'yan Boko Haram suka halaka jama'a a kauyen Faduma Kolomdi da ke karamar hukumar Gubio ta jihar Borno a ranar Talata, ya bada labarin yadda aka yaudaresu.

Mutumin, wanda ya tattauna da Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar yayin da ya ziyarci kauyen a ranar Laraba, ya ce an kashe mutane 81 tare da illata mutum 13 da kuma yin garkuwa da wasu bakwai.

Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta
Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

"Mayakan ta'addancin sun iso a motocin yaki wurin karfe 10 na safe. Sun kwashe sa'o'i shida suna ruwan wuta don sai karfe 4 na yamma suk1a bar kauyen," yace.

"Sun tattara mu da sunan za su yi mana wa'azi. Sun bukacemu da mu mika dukkan makamanmu. Wasu daga cikin 'yan kauyen sun mika wuya babu musu.

“Sun yi tamkar ba fada ya kawosu ba. Babu tsammani suka fara harbi. Hatta yara da mata ba a kyalesu ba don a take suka dinga faduwa matattu. Daga nan ne wasu suka fara gudun ceton rai.

"Tun karfe 10 na daren jiya muke birne gawawwaki har karfe 6 na safe. Mun birne gawawwaki 49 yayin da wasu 32 'yan uwansu suka tafi da su.

Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta
Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

"Yan ta'addan sun sace mutum bakwai da suka hada da dagacin kauyen. Sun sace Shanu 400 sannan suka tafi," ya kara da cewa.

A yayin martani, Zulum ya yi kira ga rundunar soji da su kara kokari wajen yaki da 'yan ta'addan.

Gwamnan ya kwatanta harin da mummunan al'amari kuma abun takauci da alhini.

KU KARANTA: Najeriya ta yi rashin shahararren dan kasuwar man fetur

"A shekarar da ta gabata, an kashe kusan mutum 80 a Gajiram. Wannan abun takaici ne da alhini. Hanyar shawo kan wannan matsalar daya ita ce halaka 'yan ta'addan da ke tafkin Chadi. Hakan na bukatar hadin guiwar yankuna," yace.

Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta
Yadda 'yan ta'adda suka yaudaremu har suka kashe mutum 80 - Mutumin da ya kubuta. Hoto daga The Cable
Asali: Twitter

Gwamnan ya kwashe mutum biyar da suka samu raunika inda ya mika su asibiti da kansa.

A wani labari na daban, rundunar sojin Najeriya ta ci gaba da yi wa 'yan bindiga ruwan wuta karkashin atisayen Operation Accord ta jiragen yaki.

A karkashin rundunar Operation Hadarin Daji, dakarun sojin saman Najeriya sun tarwatsa sansanin 'yan bindiga da ke dajin Kwayanbana a jihar Zamfara.

Dakarun sojin saman sun yi aiki ne da rahotannin sirri da suka samu wanda ya ce 'yan ta'addan na nan dankam a dajin tare da kogunan da ke kewayensa inda suka boye. A nan gagarumin dan bindiga mai suna Dogo Dede yake.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel