Aisha Buhari ta yi wa dan Atiku da ya kamu da coronavirus addu’a

Aisha Buhari ta yi wa dan Atiku da ya kamu da coronavirus addu’a

- Aisha Buhari ta yi addu’an samun lafiya ga dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda ya kamu da cutar Coronavirus

- Aisha ya aika sakon addu’a ta shafin Atiku na Twitter bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa sakamakon gwaji ya nuna dansa na dauke da cutar.

- Da farko dai Atiku ya bayyana cewa an kai dansa asibitin kwararru na Gwagwalada da ke Abuja domin samun kulawar likitoci

Uwargidar Shugaban kasar Najeriya, Aisha Buhari, a ranar Litinin, 23 ya watan Maris, ta yi wa dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar wanda sakamakon gwaji ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus addu’an samun lafiya cikin gaggawa.

Aisha ya aika sakon addu’a zuwa ga Atiku ta shafinsa na Twitter bayan tsohon mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa dansa ya kamu da cutar.

Aisha Buhari ta yi wa dan Atiku da ya kamu da coronavirus addu’a
Aisha Buhari ta yi wa dan Atiku da ya kamu da coronavirus addu’a
Asali: UGC

“Ya mai girma, tare da tarin kulawa Ina mika addu’a na don samun lafiyar danka. Allah renu en Amin,” Uwargidar shugaban kasar ta wallafa a shafin Twitter.

KU KARANTA KUMA: Annobar Coronavirus: Ka da wanda ya sake zuwa ofishin Yansanda – Sufetan Yansanda

Da farko dai mun ji cewa dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, a zaben 2019 Atiku Abubakar ya sanar da cewa ɗan sa ya kamu da ƙwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus.

Atiku ya sanar da hakan ne a shafinsa na dandalin sanda zumunta na Twitter a ranar Lahadi 22 ga watan Maris na 2020.

Ya rubuta, "Da na ya kamu da ƙwayar cutar Coronavirus."

A cewar tsohon mataimakin shugaban kasar na Najeriya, an garzaya da dan sa zuwa asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a birnin tarayya Abuja domin yi masa magani.

Ya kara da cewa, "An sanar da hukumar kula da Cututtuka masu saurin yaduwa ta Najeriya @NCDCGov kuma an kai shi asibitin koyarwa na kwararru da ke Gwagwalada a Abuja domin yi masa magani da kulawa da shi. Zan yi farin ciki idan za ku iya saka shi a addu'o'in ku. Ku cigaba da kiyaye wa domin Coronavirus gaskiya ne."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel