Shugabar wurin aikin mu ta kori ne don na ki yin zina da ita - Matashi

Shugabar wurin aikin mu ta kori ne don na ki yin zina da ita - Matashi

- Wani mutum mai suna Penjamin Franklin ya yi korafi kan yadda shugaban wurin aikinsu ta sallame shi

- Ma'abocin amfani da shafin Twitter ya ce hakan ta faru da shi domin a baya ya ki amince ya yi zina da shugaban wurin aikin su

- Penjamin ya ce ya tattauna da lauyoyinsa game da batun amma sun ce masa akwai bukatar ya nemo hujojji kafin su shigar da kara

Neman shishige wa abokan aiki abu ne da ke bata wurin aiki tare da janyo matsaloli daban-daban.

Wani mutum mai suna Penjamin Franklin ya koka kan yadda aka kafa masa kahon zuka a wurin aiki daga baya ma aka kore shi saboda kawai ya ki amincewa ya yi zina da shugaban wurin aikin su mace.

Penjamin ya ce da farko lokacin da shugaban su ta zo kusa da shi ta yi masa radi a kunne cewa yana da kuruciya ga shi ya yi sa'a a rayuwa bai dauki abin da muhimmanci ba.

DUBA WANNAN: Wa'iyazubillah: An kama wani yana zina da gawa a gaban abokinsa

Ya ce a lokacin da ya ke tunanin cewa lamarin ya zo karshe kuma za ta dena damunsa kawai zai aka kira shi aka bashi takardar sallama a kan cewa baya aikinsa yadda ya kamata.

Matashin ya ce yana zuwa aiki a kan lokaci kamar yadda ya kamata kuma babu wani abinda baya gudanarwa dai-dai gwargwado game da aikinsa.

Mutumin ya ce ya fada wa lauyansa abinda ya faru. Sai dai ya kara da cewa idan da mace ce ta yi karar cewa shugban ta na miji ya nemi ya yi lalata da ita da tuni an yarda.

Ya ce lauyoyinsa sun ce akwai bukatar ya gabatar da gamsassun hujjoji kafin su kai batun kara a kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel