Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri

Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri

Wata kungiyar addinin Musulunci dake rajin kare hakkokin Musulmai, MURIC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta dauki tsatstsauran hukunci a kan iyayen dake fatali da yayansu, musamman Almajirai mabarata.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyaa haka cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, a jahar Legas, inda yace tsarin hukunta iyayen zai sa su shiga taitayinsu game da tarbiyyar yaransu tare da basu kulawar da ta dace.

KU KARANTA: NNPC ta fara sarrafa bakin mai na Najeriya da kanta, ya shiga kasuwa

Almajiranci: Musulmai sun nemi gwamnati ta yi ma iyaye hukunci mai tsauri
MURIC da Almajirai
Asali: UGC

“Mun damu kwarai game da yawan yaran dake gararamba a kan tituna, wadannan su ne manyan gobe, yayanmu sune karfinmu, amma fa idan harm un basu tarbiyyar da ta dace ta hanyar ilimantar dasu, idan ba haka ba su zasu fitinemu.” Inji shi Akintola.

MURIC ta yi kira ga majalisar dokoki ta kasa da majalisun dokokin jaha su fara aikin samar da dokokin da zasu hukunta iyayen dake sakin yaransa sakaka, har ma ya kafa hujja da ayar Al-Qur’ani mai girma kamar haka;

“A ciki sura ta 2, aya ta 233 na Al-Qur’ani mai girma, Allah ya yi kira ga iyaye (musamman maza) su samar da muhimman bukatu kamar su abinci, wajen kwanciya, da kayan sawa, haka zalika Qur’ani ya tilasta ma iyaye su ilimantar da yaransu.

“Don haka babban sakaci da hakkin yara a kan iyaye sakin yara suna barace barace a kan titi, talla ko kuma wani aikin wahala da sunan neman kudi, bugu da kari akwai batun haihuwar yara, Allah zai tambayi iyaye yadda suka kula da yaransu.” Inji shi.

Akintola ya koka kan yadda Musulmai suka yi mummunan fahimta ga ayar Qur’ani da ta bada daman kara aure, tare da mantawa da bukatar cewa har sai yana da ikon kulawa da sauran matan da yaransu kafin ya auro su.

“Samuwar almajirai miliyan 10 a cikin babbar matsala ce, tare da nuna alamun gazawar gwamnati, yaran nan dake gararamba a kan titi matsala ne a garemu, babu yadda za’a magance miyagun ayyuka ba tare da kiyaye kananan yara ba, kama yara ba shi bane, sai dai a kama iyayensu, a daure su.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel