Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u

Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u

Shugaban kamfanin Dangote, kuma mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya kai ziyara ga abokin kasuwancinsa, AbdulSamad Rabiu, shugaban kamfanin BUA a Legas.

A yayin bayyana ziyarar, Rabiu ya nuna godiyarsa a kan wannan ziyarar da babban attajirin ya kai masa.

Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Asali: Twitter

Shugaban kamfanin BUA din ya ce: "Na yi matukar farin ciki da na karba abokina kuma dan uwana, Alhaji Aliko Dangote a ofishina a yau. Irin kudirinsa da hangensa nake amfani wajen sauya yanayin kasuwancin kasarmu Najeriya. Nagode sosai Alhaji da wannan karamcin."

Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Asali: Twitter

Babu wani dadewa, mujallar Forbes ta saki rahotonta na jerin manyan masu kudin duniya amma mutane hudu a Najeriya ne suka shiga ciki. Akwai Aliko Dangote, Mike Adenuga, AbdulSamad Rabiu da Folorunsho Alakija.

DUBA WANNAN: 'Yan agaji sun kashe 'yan bindiga 17 a Katsina, fararen hula 4 sun mutu

A cikin hudun kuwa, Dangote ne ya haye sama a matsayin babban mai kudin duniya bakar fata. Yana da arzikin dala biliyan 10.1.

Mike Adenuga shugaban kamfanin Globacom ya zo a na biyu a Najeriya kuma na uku a Afrika tare da arzikin dala biliyan 7.7.

Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Asali: Twitter

Rabiu kuwa a wannan shekarar arzikinsa ya kai dala biliyan 3.1 kuma ya zo a na takwas a jerin.

Alakija mai kamfanin Famfa Oil ta rufe jerin inda ta bayyana da arzikin dala biliyan daya kuma ta zo a ta 20 a Afrika.

Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Hotunan haduwar biloniyoyi; Aliko Dangote ya ziyarci Abdulsamad Isyaka Rabi'u
Asali: Twitter

A cikin su hudun kuwa da suka shiga jerin a wannan shekarar, Rabiu ne ya samu karuwar arziki fiye da shekarar da ta gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel