Bayan shekaru 14 da rufe ma'aikata, 'yan majalisa sun gano ana ci gaba da biyanta albashi

Bayan shekaru 14 da rufe ma'aikata, 'yan majalisa sun gano ana ci gaba da biyanta albashi

Wani kwamitin majalisar wakilai a ranar Litinin, ya gano cewa bayan shekaru 14 da aka yi da kulle hukumar hako ma'adanai ta Najeriya, ma'aikatan na ci gaba da karbar albashi daga gwamnati.

Shugaban kwamitin, Oluwole Oke, ya umarci ministan ma'aikatar ma'adanai da karafa, Olamilekan Adegbite, Ministan ruwa, Suleiman Adamu da daraktan hukumar aiyukan gwamnati, Alexander Okoh da su gurfana gaban kwamitin.

Adegbite da Okoh zasu yi bayanin dalilin da yasa ma'aikatan cibiyar gwamnatin da aka rufe tun 2006 suka ci gaba da karba daga dukiyar gwamnati.

Mataimakin babban manajan sashin kudi na hukumar hako ma'adanan, Dauda Gambo, ya sanar da kwamitin cewa an rufe hukumar ne sakamakon komawa da za ta yi mai zaman kanta tare da hadin guiwar BPE.

Bayan shekaru 14 da rufe ma'aikata, 'yan majalisa sun gano ana ci gaba da biyanta albashi
Bayan shekaru 14 da rufe ma'aikata, 'yan majalisa sun gano ana ci gaba da biyanta albashi
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mai farin jini: Dubban jama'a sun yi tururuwar fitowa domin tarbar Buhari a Ondo (Hotuna)

Hakazalika, kwamitin ya gano cewa kusan tsoffin ma'aikatan kasuwar duniya ta Legas 24 wadanda aka kora suke ci gaba da karbar albashi daga hukumar.

Kwamitin ya mika takardar tuhuma ga RBDA don jin dalilin da ya hana su mika yadda suka kashe kudinsu ba, ga ofishin babban oditan tarayya.

Kwamitin ya kara da barazanar bada umarnin damko duk wani shugaban ma'aikata, bangare ko cibiya karkashin gwamnatin tarayya, wacce ta kasa bayyana gabanta don kare yadda ta kashe kudinta.

Oke ya sanar da wannan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin a kan zargin wasu cibiyoyi da boye-boye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel