Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, ya shiga taro na musamman tare da sifeta janar na 'yan sanda da shugabannin tsaron kasar nan. An yi taron ne a fadar shugaban kasa a Abuja, babban birnin tarayya.

Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban tsaro Janar Gabriel Olonisakin, shugaban rundunar sojin Najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai, shugaban sojin sama, Air Marshall Sadique Abubakar, shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas.

Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Asali: Twitter

Sifeta Janar din 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya samu damar halartar taron, wanda aka yi yayin da ake tsaka da fuskantar kalubalen tsaro a kasar nan.

Amma kuma mai bayar da shawara a kan tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, baya nan.

Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Asali: Twitter

Buhari da shugabannin tsaron suna yin taruka a kan tsaro kusan kowanne mako, amma dai na yau an kirasa da na musamman.

Shugabannin tsaron sun wuce ta ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasar, Abba Kyari, a yayin da suke ficewa bayan kammala taron.

Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Asali: Twitter

Buratai ne na karshe da aka gani ya bar wajen da misalin karfe 3:55 na yamma.

A cikin kwanakin nan ne aka matsantawa Buhari a kan ya sallami shugabannin tsaron kasar nan sakamakon kalubalen tsaron da kasar nan ke ci gaba da fuskanta.

Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Asali: Twitter

Hatta majalisar dattijan kasar nan sun yi kira ga shugaban kasar a kan ya sallami shugabannin tsaron.

Amma kuma, har yanzu shugaban kasar yayi biris da wannan kiran, tare da cewa mulkinsa ba zai dau mummunan mataki a kan shugabannin tsaron da suka dinga kokari tun 2015 ba.

Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Buhari ya shiga ganawa ta musamman da shugabannin hukumomin tsaro, babu Monguno (Hotuna)
Asali: Facebook

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel