Jami’ar BUK ta karrama wata Baturiya da ta kwashe shekaru 50 tana koyar da harshen Hausa

Jami’ar BUK ta karrama wata Baturiya da ta kwashe shekaru 50 tana koyar da harshen Hausa

Jami’ar Bayero ta Kano ta shirya wani babban taro a kan harshen Hausa domin karrama wata baturiya yar kasar Poland, Farfesa Nina Pawlak da ta kwashe tsawon shekaru 50 tana bincike tare da karantar da harshen Hausa a jami’a.

Jaridar Kano Focus ta ruwaito Pawlak tana koyarwa ne a jami’ar Warsar dake Poland, kuma ta yaye dalibai a matakin digiri na uku da suka hada da Hafizu Miko Yakasai da Isah Yusuf Chamo, haka zalika ta tantance wani babban Malamin Hausa a BUKM Farfesa Yakubu Magaji Azare.

Jami’ar BUK ta karrama wata Baturiya da ta kwashe shekaru 50 tana koyar da harshen Hausa
Pawlak
Asali: Twitter

Cibiyar bincike a kan harsunan Najeriya ta jami’ar Bayero ce ta shirya taron na kwanaki biyu. Da yake kaddamar da taron a ranar Talata, shugaban jami’ar BUK, Farfesa Yahuza Bello ya bayyana Pawlak a matsayin hamshakiyar masaniya, wanda ta sadaukar da rayuwarta ga bincike da karantar da harshen Hausa.

“Ina farin cikin mika godiyar jami’ar BUK gare ki bisa gudunmuwar da ki ka bamu, musamman wajen horas da manyan malamanmu, da kuma alakar da ki ka kulla tsakaninmu da manyan cibiyoyi da jami’o’I, da kuma littafan da ki ka buga, da ma ziyarar da ki ka kawo mana da kuma kyakkyar tarba da ki ke bamu idan mun ziyarce ki.

“Ina mika miki godiyar daliban mu da malamanmu bisa ilimin da ki basu, sa’annan ina mika godiya a madadin al’ummar Hausa gaba daya bisa gudunmuwar da ki ke bayarwa wajen cigaban harshen a Duniya.” Inji shi.

A nata jawabin, Farfesa Pawlak ta bayyana cewa ta sadaukar da lokacinta wajen karantar harshen Hausa ne saboda kara fahimtar juna tsakanin kasasheh Afirka da kasashen nahiyar Turai.

“Idan na yi murabus daga aiki a shekara mai zuwa, zan rubuta kamus na kalmomin Hausa da na harshen Polish domin dalibai masu koyon Hausa a Poland.” Inji ta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel