Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a gidan David Mark a Benue

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a gidan David Mark a Benue

Gobara ta yi barna a gidan tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Marki da ke garin Otukpo a jihar Benue a ranar Alhamis kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Wasu da abin ya faru a idanunsu sun ce gobarar ta yadu ne daga wani daji da ke kusa da katangan gidan tsohon shugaban majalisar inda ta kone motoccin daukan marasa lafiya biyu da fiye da babura 15 da ke harabar gidan.

An bayyana cewa masu aikin gidan sun yi kokarin kashe gobarar amma ba su yi nasara ba kafin daga bisani ma'aikatan kwana-kwana na Otukpo suka iso wurin suka taimaka.

DUBA WANNAN: 2023: Ɗankwambo ya aike wa 'yan PDP saƙo

Daya daga cikin ma'aikatan gidan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, "munyi iya kokarin mu don ganin mun kashe gobarar amma duk da haka ta cigaba da yaduwa.

"Da muka gano ba za mu iya kashe gobarar bane kuma za ta kama gidan saukan baki sai muka kira jami'an kwana-kwana."

A lokacin rubuta wannan rahoton, babu wani iyalan gidan tsohon shugaban majalisar dattawan da ya yi tsokaci a kan lamarin duk da cewa an gano David Mark kansa baya gida a lokacin da abin ya faru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel