Rukunin wayoyin hannu da manhajar 'WhatsApp' zata daina aiki a 2020

Rukunin wayoyin hannu da manhajar 'WhatsApp' zata daina aiki a 2020

Kamfanin WhatsApp ya ce manhajarsa zat dena aiki a wayoyin da suka kai shekaru biyar da kerawa. WhatsApp din wanda mallakin Facebook ne ya daina aiki a kan wayoyi kirar windows wadanda Operating System din su ya tsufa tun daga ranar 31 ga watan Disamba na 2019.

Wannan matakin zai shafi wayoyi samfurin Nokia Lumia ne wadanda suke amfani da manhajar Windows.

Wayoyi irinsu Nokia Lumia 65 sun shuga kasuwa ne shekara hudu da suka gabata, amma kuma har yanzu ana mafani dasu.

Daga watan Fabrairu na sabuwar shekarar nan, wannan lamarin zai shafi wayoyi kirar Iphone wadanda ke amfani da manhajar iOS 8 da kuma wayoyi kirar Android dake amfani da manhajar 2.3.7.

Tun a daya ga watan Yuli ne mutanen dake amfani da irin manhajar Microsoft wajen sauke manhajoji a wayoyinsu suka daina sauke WhatsApp a wayoyinsu.

DUBA WANNAN: Kaduna: Gobara ta kone mai jego, jariri da mutane uku a Rigasa

Hakan kuma ya zo ne bayan kamfanin na WhatsApp ya gargadi masu amfani da shi kan wayoyinsu na Windows cewa za su lura wani bangare na WhatsApp din ya daina aiki a wayoyinsu.

WhatsApp ya ce duk da matakin ba abin da suka so bane amma hakan shi ne zai sa su bai wa mutane damar sada zumunci da 'yan uwansu.

Idan zamu tuna, a shekarar 2018, WhatsApp ya daina aiki a wayoyi samfurin BlackBerry da kuma wadanda manhajarsu ta Window ta zama tsohon yayi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel