Za a samu karancin abinci da kudi a 2020 – Babban Fasto

Za a samu karancin abinci da kudi a 2020 – Babban Fasto

Shugaban cocin Living Christ Gospel, a Najeriya da kasar waje, Dr Nathaniel Olorunsho, ya bayyana cewa akwai bukatar yan Najeriya su yi addu’a da azumi domin karkatar da annobar da ke shekarar 2020 sannan kuma su kasance cikin alkhairan sabuwar shekarar.

Olorunshola, wanda ya bayyana cewa “Ubangiji ya ce akwai daidaito tsakanin alkhairi da sharri a shekarar,” ya bayar da tabbacin cewa Ubangiji na da tarin alkhairai ga yan Najeriya, cewa “kowa ya fara shekarar da azumi da addu’a na tsawon kwana bakwai domin alkawarin Allah ya tabbata.”

Faston wanda ya yi magana a hedkwatar cocin da ke Ado-Ekiti, jihar Ekiti a yayin gabatar da littafin wahayinsa na 2020 a ranar Talata ya ce, “za a samu karancin abinci a 2020 wanda hakan zai haddasa tsadar kayayyakin abinci sosai.

“Za a samu karancin kudi daga Janairu zuwa Yuni. Sai dai kuma lamarin zai inganta daga tsakiyar shekarar zuwa karshen shekarar.

KU KARANTA KUMA: Ma’aikatan jihar Katsina za su fara cin moriyar sabon karancin albashi daga Janairun 2020

“Za a samu rikicin siyasa daban-daban. Kungiyoyin kwadago harda malaman jami’a Za su tafi yajin aiki. Kafin fara biyan sabon karancin albashi, zai zaman abubuwa da dama sun faru.

“Farkon shekarar 2020 zai kasance mai wahala. Shawarana ga mutane shine su yi tanadi,” inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel