A yayin da ake rade- radin mutuwarsa, IBB ya bayyana shirinsa na yin aure bayan shekara 10 a matsayin gwauro

A yayin da ake rade- radin mutuwarsa, IBB ya bayyana shirinsa na yin aure bayan shekara 10 a matsayin gwauro

Tsohon shugaban kasar Najeriya a mulkin soji, janar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya shafe tsawon shekaru 40 yana zaune tare da matarsa, marigayiya Maryam Babangida, kafin mutuwarta a watan Disamba na shekarar 2009.

Marigayiya Maryam ta yi suna a Najeriya saboda irin tasirin da take da shi a kan mijinta da kuma soyayyar dake tsakaninsu. Kusan duk inda IBB yake yana tare da marigayiya Maryam, tamkar 'Zara' da 'Wata'.

A wata tattauna wa da jaridar 'The Sun' ta yi da IBB kuma ta wallafa a ranar Asabar, 28 ga watan Disamba, IBB ya bayyana cewa har yanzu bai daina jin radadin mutuwar Maryam ba duk da tsawon lokacin da ya shude tun bayan komawarta ga mahaliccinta.

Sai dai, duk da irin kewarta da jin radadin rayuwa babu Maryam a tare da shi, IBB ya bayyana cewa yana son zai sake yin aure.

IBB ya kara da cewa da gaske yake yi yana son zai sake yin aure saboda tsufa yake kara yi, a saboda haka akwai lokacin da bukatar abokiyar zama ba zai yi masa wata rana ko amfani ba.

Da wakilin jaridar 'The Sun' ya tambaye shi a kan koda gaske yana son sake yi aure ko kuma dai fada kawai yake yi kawai da wasa, sai IBB ya ce, "har yanzu amsa ta a kan batun aure bata sauya ba, watau 'Eh' ina da niyyar sake aure, kawai ina tunani ne har yanzu a kan lamarin."

Da aka tambaye shi ko akwai wata da yake burin aure a halin yanzu, sai IBB ya amsa da cewa, "a'a, ni babu wata mace a raina da nake buri ko fatan aure, amma tabbas ina da niyyar sake yin aure saboda kullum tsufa nake kara yi, idan ban yi aure kwana kusa ba, zan wuce lokacin da zai yi min amfani."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel