Gwamna El-Rufai zai kashe N100m wajen gyaran gidajen mari a Kaduna

Gwamna El-Rufai zai kashe N100m wajen gyaran gidajen mari a Kaduna

Dazu nan mu ka samu labaro cewa Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi na’am da kashe kudi Naira miliyan 100 domin a gyara gidajen marin da ke cikin jiharsa.

El-Rufai ya amince da wannan mataki ne bayan kiran da Iyayen yara su ka rika yi wa gwamnatin Kaduna na ta samar da wuraren da za a killace yaran da su ka kangare domin ayi masu tarbiya.

Mutane 13 da aka karbo daga gidajen mari a jihar Kaduna su na babban asibitin kwakwalwa na tarayya da ke cikin birnin jihar domin a duba lafiyar kansu kamar yadda TVC ta bada rahoto.

Yayin da wasu ‘Yan marin su ka dawo gidajensu gaban ‘yanuwa da abokai, wasu sun zama ala-ka-kai a dalilin kangarewar da su ka yi, wannan ya sa iyayensu, su ka rasa yadda za su yi da su.

KU KARANTA: Majalisa ba ta goyon bayan a haramta shigo da na'urorin bada wuta

Kwamishinar cigaban al’umma da harkokin jama’a, Hafsat Baba, ta bayyana cewa gwamnati ta na kokari domin biyan bukatun wadannan Bayin Allah da su ke kira a gina lafiyayyun gidajen horo.

An gurfanar da wadanda su ke kula da gidajen marin da aka bi aka rufe a jihar, amma sun fadawa kotu cewa babu laifin da su ka aikata domin hukuma ta ba su duk takardun iznin da ake bukata.

Wasu daga cikin mutanen da aka dauke daga wadannan gidaje na mari su na kokarin nunawa Duniya cewa babu wani alheri ko abin da za a karu da shi a irin wadannan gidaje na Malam-Niga.

Iyaye sun musanya hakan, inda su ka bukaci gwamnati ta gyara wadannan gidaje domin a tsare yaran har sai sun gyaru. Gwamnatin Kaduna ta amince da maida gidajen kirar ginin zamani.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel