Dakarun NAF sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa

Dakarun NAF sun tsallake rijiya da baya bayan jirginsu ya yi saukar gaggawa

- Dakarun sojin saman Najeriya (NAF) sun tallake rijiya da baya yayin da jirgin su ya kusa yin hatsari

- Jirgi yakin na NAF yana dauke ne da sojin ya yi saukar gaggawa a jihar Enugu

- Shugaban NAF ya bukaci al'umma su cigaba da bawa rundunar goyon baya yayin aikin ta na samar da tsaro

Jirgin sojin saman Najeriya ya yi saukar gaggawa a jihar Enugu. Jirgin dauke da sojojin ya yi saukar gaggawa ne bayan jerin ayyukan da ya yi a yau Alhamis 14 ga watan Nuwamban 2019.

An auna arziki dai babu wanda ya rasa ransa ko ya samu rauni daga cikin sojin ko kuma mutane da ke wurin da jirgin ya yi saukar gaggawar.

DUBA WANNAN: Aisha Buhari ta fadi abinda ya hana Gwamna Bello biyan albashi a watannin a baya

Mai magana da yawun rundunar sojin saman, Air Commodore Ibikunle Daramola ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter.

Kamar yadda yace, shugaban rundunar sojin saman, A. M. Sadique ya bayar da umarnin kafa kwamiti ta musamman na bincike don gano dalilin hatsarin.

Rundunar sojin saman ta Najeriyan na neman fahimtarku da goyon bayan al'umma, a kan yadda ta ke kokarin ganin tabbatar tsaro ga Najeriya da 'yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel