A wajen kananan yara nake samun gamsuwa, in ji wani dan luwadi

A wajen kananan yara nake samun gamsuwa, in ji wani dan luwadi

- 'Yan sandan jihar Niger sun cafke wani mutum mai shekaru 35 da laifin yaudarar yara masu kananan shekaru yana luwadi da su

- Asirinsa ya tonu ne bayan da ya lalata wani yaro mai shekaru 8 kacal a duniya

- Ya bayyanawa hukumar 'yan sandan cewa, a tare da kananan yaran ne yake samu gamsuwa

Hukumar 'yan sandan jihar Niger, ta cafke wani mutum mai shekaru 35, mai suna Ahmed Isah da laifin luwadi da kananan yara.

Isah, wanda ke zama a Sarkin-Pawa a karamar hukumar Munya ta jihar Niger, ya shiga hannun 'yan sandan ne bayan da suka samu rahoton yadda ya yaudari wani yaro mai shekaru 8 har ya lalatashi.

Wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma ya tabbatar da cewa a wajen yara masu shekaru 8 zuwa 10 ne yake gamsuwa.

DUBA WANNAN: APC ta fallasa wani makirci da Atiku da PDP ke shiryawa alkalan kotun koli

Kamar yadda yace, yana yaudarar yaran ne da biskit, minti da sauran kayan kwalama da makulashe don toshe bakinsu kada su sanar da iyayensu aika-aikar.

Ya bayyana cewa, ya yi kusan shekaru uku kenan a wannan harkar saboda bashi da kudin da zai samu budurwar da zai rage zafi da ita.

"Na fada wannan harkar ne saboda bani da kudin da zan bawa mata in rage zafi. Kuma basu bada jikinsu kyauta. Don haka ne na fada harkar luwadi da kananan yara,"

Ya kara da cewa, "Mun dade da rabuwa da budurwata saboda bana bata kudi bayan mun gama jima'i. Tace bazata iya bani kyauta ba."

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, Muhammad Abubakar, wanda ya cafko wanda ake zargin a ranar Talata, ya hori iyaye dasu ilimantar da yaransu akan hadurran Dame kunshe da irin wannan harkar.

"Akwai bukatar mu saki jiki da yaranmu don su samu fuskar sanar damu irin wadannan kalubalen a kowanne lokaci idan suka tunkarosu. Abin bakin ciki ne ace yaro na fuskantar wannan kalubalen amma ba ya iya sanar da iyayensa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel