Allah sarki: Tsohuwa ta dage tana faman zabga bara ga wani mutum-mutumin roba a tunanin ta mutum ne

Allah sarki: Tsohuwa ta dage tana faman zabga bara ga wani mutum-mutumin roba a tunanin ta mutum ne

Yanzu haka wani hoto wata tsohuwa ne yake ta yawo a shafukan sada zumunta, inda aka ganta a bakin wani shagon sayar da kaya tana yin bara ga irin mutum-mutumin nan da ake yin tallar kaya da shi tunaninta mutum ne

Kowa ya san cewa matsalar talauci na cigaba da kara ta'azzara a Najeriya, hakan ya sanya mabarata suka kara yawa a titunan kasar nan.

Yanzu haka akwai hotunan wata tsohuwa da suke ta yawo a shafukan sadarwa, wadanda suka bawa mutane da yawa tausayi, domin kuwa an nuno tsohuwar ne tana bara a bakin wani shago.

A hotunan wandanda sun riga sun gama yawo a shafukan sadarwa, matar ba wai tana yin bara ga mutum bane, sai dai an nuno ta tana ta faman zabga bara ga irin mutum-mutumin nan da ake tallar kaya da shi a kofar shagunan sayar da kayan sawa.

Za'a iya cewa tsufa ko rashin gani ne ya sanya ta kasa gane cewa abin nan ba wai mutum bane, mutum-mutumi ne na roba.

KU KARANTA: Allah mai iko: An haifi wani jariri babu fuska a kasar Portugal

A lokacin da mutane da yawa suka zage karfinsu da lokutan su domin ganin sun cimma burinsu na rayuwa, wasu kuwa tuni sun riga sunyi nisa wajen jin dadi na rayuwa, hakan ya biyo bayan wani mutumi da ya mutu a sanadiyyar hadarin mota.

Mutumin mai suna Syvanus Okpanachi, mai shekaru 40 a duniya, kwanan nan ya samu aikin yi bayan shafe shekaru da dama yana ta fama bai samu ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel