Hotunan gangariyan sabbin jiragen kasa na zamani da China ta kera wa Najeriya

Hotunan gangariyan sabbin jiragen kasa na zamani da China ta kera wa Najeriya

Ministan Sufuri Chibuike Rotimi Ameachi a daren jiya Alhamis 17 ga watan Oktoban 2019 ya wallafa hotunan sabbin jiragen kasa na zamani da gwamnatin tarayya tayi oda daga kasar China.

Ameachi ya tafi kasar China da kansa domin duba ingancin jiragen da ya ce za su iso Najeriya cikin dan kankanin lokaci.

A cewar Ministan an kammala kashi na farko na jiragen da suka hada da jiragen kasa masu dan karen kudu na zamani 2 da kuma jiragen kasa (Locomotive) guda hudu.

Ya kuma ce tuni an fara aiki kan jiragen kashi na biyu. Ya ce gwamnatin tarayya tana son sada dukkan jihohin kasar ne ta hanyar dogo.

DUBA WANNAN: 'Yan asalin jihar Filato sun cacaki Gwamna Lalong saboda ya nada bahaushe mukami

Ya yi kira da al'ummar kasar su bawa gwamnati hadin kai da goyon baya domin more romon tsarin mataki na gaba na gwamnati wato #Next Level.

Ga hotunan sabbin jiragen a kasa.

An zaga da ministan cikin daya daga cikin jiragen inda ya ce wadanda ke kukan karancin jiragen kasa daga Kaduna zuwa Abuja da Legas zuwa Ibadan su sha kuruminsa domin gwamnati ta ji kukan su kuma za ta share musu hawaye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel