Akwai yuwuwar barkewar cutar tetanus a jihohi 11 na arewacin Najeriya, UN

Akwai yuwuwar barkewar cutar tetanus a jihohi 11 na arewacin Najeriya, UN

- Majalisar dinkin duniya tace akwai yuwuwar barkewar cutar tetenus a jihohi 11 na arewacin Najeriya

- Yankin kudu maso gabas ne ke da yuwuwar samun kaso mafi yawa na masu cutar

- Kananan hukumomi 138 ne annobar zata shafa a arewacin Najeriya, in ji majalisar

Majalisar dinkin duniya ta ce akwai yuwuwar barkewar cutar tetanus a jihohi 11 na arewacin Najeriya

Dr. Idris Nagya,ma’aikaci da majalisar ne ya sanar da hakan a taron wayar da kai a Minna.

Yace yuwuwar barkewar annobar ta shafi kananan hukumoi 138 tare da jaddada cewa za afi samun masu cutar a yankin arewa maso gabas na kasar nan.

KU KARANTA: Lawan ya bawa ministoci wa'adin kare kasafin kudin ma'aikatunsu

Cutar tetanus mummunar cutar ce da zata iya zama ajalin wanda ya kamu da ita.

Kamar yadda yace, kananan hukumomin jihar Neja da akwai yuwuwar barkewar cutar sun hada da: Agwara, Edati, Magama, Mashegu, Mokwa, rafi da Shiroro.

Nagya ya danganta hakan da yawaitar rashin ilimi, al’adu da addini, rashin isassun cibiyoyin kiwon lafiya wadanda yakamat masu ruwa da tsaki su shawo kai.

Daraktan rigakafin cibiyoyin lafiya na jihar Neja, Dr. Fati Sheik Abdullah, ta bayyana cewa akawi yuwuwar wayar da kan da ake akan cutar tetanus a Najeriya ta yi amfani da yawa sakamakon kokarin da kafafen yada labarai ke yi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel