Kuda wajen kwadayi ake mutuwa: Mijin matar da yake bibiya ya hallakasa har lahira

Kuda wajen kwadayi ake mutuwa: Mijin matar da yake bibiya ya hallakasa har lahira

- Hukumar 'yan sandan jihar Delta ta tabbatar da cafke wani mutum da kaninsa a zargin da take musu na kashe masoyin matarsa

- Duk da matar ta sanar da shi tana da aure, Ukrakpo bai daina bibiyarta ba da nuna mata kauna

- Bayan soka masa wuka da suka yi, sai da suka bi jikinsa da yaji don tabbatar da mutuwarsa

Hukumar 'yan sandan jihar Delta ta tabbatar da kisan gillar da aka yiwa Pius Ukrakpo sakamakon zarginsa da ake da bin matar wani a yankin Jeddo da ke karamar hukumar Okpe a jihar Delta.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sandan, Onome Onovwakpoyeya ya tabbatar wa da jaridar Tribuneonline faruwar hakan a tattaunawar wayar tafi da gidanka a yammacin ranar Laraba.

DSP Onovwakpoyeya, ya ce mijin matar ya halaka Pius ne da taimakon kaninsa kuma 'yan sanda sun cafkesu tare da tuhumarsu da laifin kisan kai.

Mijin matar ya sokawa marigayi Ukrakpo wuka ne inda ya kaisa har lahira.

Lamarin ya auku ne a titin asibiti da ke Jeddo.

KU KARANTA: Sabbin kirkire-kirkire ne hanyar inganta aikin gwamnati, in ji Yemi-Esan

Mama Ejime ta sanar da Ukrakpo cewa tana da aure amma sai ya yi kunnen uwar shegu da zancenta inda ya cigaba da bayyana mata irin kaunar da yake mata. Mama Ejime ta yaudaresa zuwa gidanta inda mijinta da kaninsa ke jira don yin aika-aikar.

A tunanin Ukrakpo ya samu damar da ya dade yana nema, ashe kuwa bai san ajalinsa zai tarar ba.

Mama Ejime ta rufe kofar gidanta don tabbatar da hakarsu ta cimma ruwa. Bayan mazajen sun soka masa wuka, sai suka bi jikinsa da dakakken yaji har sai da suka tabbatar ya mutu har lahira.

Majiya da dama sun ji kuwwa da kururuwar Ukrapo amma kafin su iso ya mutu. Mama Ejime kuwa tuni ta tsere.

Labarin mummunan lamarin ya kai kunnen 'yan sintiri ne inda suka je har gida tare da tisa keyar wadanda ake zargin har gaban 'yan sanda.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel