Mutane 6 sun mutu yayin da Tirela ta wuntsula a gadar Gombe

Mutane 6 sun mutu yayin da Tirela ta wuntsula a gadar Gombe

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, wata babbar motar tirela makare da kwanukan rufin gida ta afka ma wasu tarin motoci, babura da a daidai sahu a akan gadar Doma dake jahar Gombe, wanda tayi sanadiyyar mutuwar mutane 6.

Gidan talabijin ta Channels ta ruwaito an hangi wata babbar motar Hummer mai cin mutane 18 ta makale a karkashin tirelar, haka zalika tirelan ta tattake sauran babura da a daidai sahu, inda a nan mutane 6 suka mutu.

KU KARANTA: Ta Allah ta yi: Cutar shawara ta halaka wani gagararren mai garkuwa da mutane a Zamfara

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jama’a masu bada agaji sun garzaya da mutane 10 da suka samu munana rauni zuwa asibiti. Shi ma kaakakin rundunar Yansandan jahar, DSP Nasiru Muhammad ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A cewar Nasiru, Tirelan ce ta yi ciki da motar Hummer Bus, wanda ita kuma ya afka ma motar diban yashi, da haka ne hatsarin ya rutsa da babura da wasu a daidai sahu guda biyu, duk a akan gadar Doma dake hanyar Gombe zuwa Biu.

A wani labarin kuma Wani gagararren dan bindiga daya shahara wajen satar mutane tare da yin garkuwa dasu a jahar Katsina da Zamfara, Alhaji TK ya gamu da ajalinsa a dalilin barkewar cutar shawara.

Cutar shawara ce ta yi ajalin TK tare da mukarrabansa guda 11, inda ta kara da cewa TK yana da yara yan bindiga sama da 200 da suka mamaye dajin Birnin Gwari, Sabuwa, Faskari, Danmusa, Jibiya har zuwa Nijar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel