Gwamnatin tarayya za ta aiwatar da ayyukan wutar lantarki a jami’o’i 37 - Buhari

Gwamnatin tarayya za ta aiwatar da ayyukan wutar lantarki a jami’o’i 37 - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace gwamnatinsa ta kaddamar da ayyukan wutar lantarki a jami’o’in tarayya 37 a fadin Najeriya.

Buhari ya fadi haka ne a lokacin bikin yaye dalibai na jami’ar Tarayyar dake Otuoke, a karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa.

Yayin da ya samu wakilcn mataimakin babban Sakataren kungiyar jami'o'in Najeriya, Dr Ramon Yusuf Suleiman, Buhari yace shirin bunkasa wutar fannin ilimin zai amfani dalibai 129,000 da kuma wutar hanyoyi guda 2850 idan aka kammala.

Yace Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da biyu daga cikin wadannan ayyukan, daya a jami’ar tarayyar ta Alex Ekueme da wani a Babbar jami’ar Bayero.

Yace: “Ba zan gaza ambaton cewa daya daga ciki manufofinmu a cibiyoyin ilimin jami'a shine magance matsalar rashin isasshen wutar lantarki a manyan cibiyoyin karatu.”

KU KARANTA KUMA: Babu wata matsala Dan kujerar shugaban kasa ta cigaba da zama a arewa a shekarar 2023 - Ango Abdullahi

A wani labarin kuma mun ji cewa guda daga cikin shuwagabannin kungiyar dattawan Arewacin Najeriya, Dakta Hakeem Baba Ahmed ya fallasa mutanen dake mayar da agogon baya ga cigaban Arewa, inda yace shuwagabannin Arewa ne matsalar Arewa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito Hakeem ya bayyana haka ne yayin wani taron kaddamar da reshen dalibai na hadaddiyar kungiyar kungiyoyin Arewa a jami’ar Bayero dake jahar Kano, inda yace shuwagabannin Arewa basu damu da cigaban yankin ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel