Alkalin alkalan Najeriya zai rantsar da sabbin manyan lauyoyi a kotun koli

Alkalin alkalan Najeriya zai rantsar da sabbin manyan lauyoyi a kotun koli

- A ranar Litinin mai zuwa, 23 ga watan Satumba ne alkalin alkalan Najeriya zai rantsar da sabbin manyan lauyoyi

- Rantsarwar na daga cikin jerin al'adun da ke nuna farawar sabuwar shekarar shari'a

- Alkalin alkalan zai yi jawabi akan aiyukan kotun kolin tare da ma'aikatar shari'a baki daya

A ranar Litinin mai zuwa, 23 ga watan Satumba, alkalin alkalan Najeriya, Muhammad Tanko, zai rantsar da sabbin manyan lauyoyin Najeriya 38 a kotun koli.

A takardar da daraktan yada labarai na kotun koli, Festus Akande, ya sa hannu, ya ce bikin rantsarwar na daya daga cikin jerin al'adun shekarar shari'a ta 2019/2020.

Kamar yadda Akande ya sanar, na daga cikin al'adar kotun kolin ne babban alkalin zai bada rahoton halin da ma'aikatar shari'ar ta ke ciki.

KU KARANTA: Damuwa a fadar shugaban kasa a kan makomar mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo

Ya kara da cewa jawabin zai bada gaske ne akan kokarin kotun koli har ma da ma'aikatar shari'ar a shekarar 2018 zuwa 2019.

Idan zamu tuna, cikin lauyoyi 117 da suka bukaci karin girma zuwa mataki zuwa manyan lauyoyin Najeriya a 2019, 38 ne kacal daga ciki suka yi sa'ar tsallake tantancewar.

Daraktan ya kara da bayyana cewa a cikin 38 din, 3 daga ciki malaman makaranta ne sai 35 kuma daga cikin lauyoyin kotu ne.

"Za a fara bikin bude sabuwar shekarar shari'a da karfe 10:00 na safe," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel