Wani matashi ya sace babur din danuwansa kuma ya aika shi lahira

Wani matashi ya sace babur din danuwansa kuma ya aika shi lahira

Rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti ta bamu labarin cewa ta samu nasarar kama wani matashi dan shekara 24 mai suna Ebenezer Olorunleke wanda ya kashe danuwansa tare da taimakon abokansa uku inda suka sace masa babur da wasu kayayyakinsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Asuquo Amba da yake zantawa da manema labarai game da wannan lamarin ya ce wanda ake tuhumar ya fito ne daga karamar hukumar Jege ta jihar Kogi. Ana zarginsa da laifin kisan danuwansa ta hanyar amfani da wuka da kuma sukundireba a ranar 29 ga watan Agusta, 2019.

KU KARANTA:Kotu ta bada izinin a kamo wani dan Majalisar Jihar Bauchi

Kwamishinan ya kara da cewa, sauran abokan matashi guda uku ne suka yiwa gidan danuwan nasa kawanya inda suka daba masa wuka kuma suka yi gaba da jan babur dinda kirar Bajaj mai lamba ADK 100 UJ.

Abubuwan da aka samu a hannun wanda ake tuhumar sun hada da, wuka, sukundireba da kuma babur kirar Bajaj.

“Daba masa wuka sukayi a ciki suka tsinka masa ‘ya’yan hanji a lokacin da matarsa da diyansa ba su gidan. Matashin ya amsa cewa ya aikata wannan laifin.” Inji kwamishinan.

A wani labarin mai kama da wannan kuwa zaku ji cewa an samu barkewar wani hargitsi a tsakanin kungiyar IMN wadda aka fi sani da shi’a da kuma ‘yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ranar Talata yayin da suka fito domin yin tattaki na yinin ashura.

Majiyar Daily Trust ta ruwaito mana cewa mabiya kungiyar ta shi’a dai sun yi biris ne dokar da gwamnati ta sanya masu na haramta masu yin irin wannan fita, tun a lokacin da kotu ta bayyana kungiyar a matsayin kungiyar ta’addanci.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel