Dokar hana barace-barace: Hukumar Hisbah ta kama mabarata 46 a Kano

Dokar hana barace-barace: Hukumar Hisbah ta kama mabarata 46 a Kano

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mutane 46 wadanda ake zarginsu da laifin yin barace-barace a kan tituna kasancewar gwamnatin jihar ta sanya hakan a matsayin doka.

Mai magana da yawun hukumar Hisban, Lawan Ibrahim ne ya bada wannan sanarwar a cikin wani zancen da ya fitar ranar Juma’a a Kano.

KU KARANTA:El-Rufai vs Shehu Sani: Kwanan El-Rufai 3 a Abuja yana rokon Buhari ya tafi da shi Japan – Shehu Sani

A cewarsa, an kama mabaratan ne a ranar Alhamis da rana tsaka a sakamakon wani samame da ma’aikatan hukumar suka kai a tsakanin Sakatariyar Audu Bako, gidan Biredin Oasis, shiyyar Tarauni, titin Magwan da na Iyaka da ke cikin kwaryar birnin Kano.

“Mutum 32 daga cikinsu manyane wadanda suka kai shekarun balaga yayin da 14 kuma yara ne kanana. Zamu zaunar da su domin yi masu bayani a kan dokar haramta bara a bisa tituna da gwamnati ta sa daga nan kuma sai mu sake su saboda wannan shi ne karo na farko da muka kama su.” Inji kakakin.

Kamfanin dillacin labaran Najeriya ya kawo mana rahoton cewa a ranar Laraba 28 ga watan Agusta hukumar ta kama wasu mutum 60 da laifin yin bara a bisa titunan birnin Kano abinda gwamnatin jihar ta haramta.

A wani labarin makamancin wannan kuwa zaku ji cewa, ‘yan gudun hijra 25,000 sun koma zuwa garuruwansu a jihar Zamfara.

Shugaban hukumar bayar da taimakon gaggawa ta jihar Zamfara wato ZEMA, Alhaji Sanusi Kwatarkwashi ne ya bayar da wannan labari ranar Juma’a a Gusau lokacin da yake zantawa da manema labarai a kan cigaba da jihar ta samu na bangaren tsaro.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel