Attajiri, Alhaji Hussaini Bokane, ya taimakawa jihar Bauchi da kayayyakin asibiti na kimanin N250m

Attajiri, Alhaji Hussaini Bokane, ya taimakawa jihar Bauchi da kayayyakin asibiti na kimanin N250m

Wani babban attajiri, Alhaji Hussaini Bokane, ya baiwa gwamnatin jihar Bauchi sadakan kayayyakin asibiti na kimanin kudi milyan dari biyu da hamsin.

Ya bayyana cewa ya yi wannan taimako ne saboda talakawa da marasa galihu a karkara da biranen jihar ba su samun isassahen kiwon lafiya a asibitocin jihar.

Alhaji Hussaini Bokane, wanda shine shugaban kamfanin Lautech Solutions Limited dake Abuja ya ce yawancin asibitocin gwamnati ba su da kayayyakin da suke bukata wajen kula da marasa lafiya.

Hakazalika, ya ce wannan gudunmuwa da ya bayar zai taimakawa gwamnatin wajen dakile wasu kalubalen da bangaren kiwon lafiya ke fama da shi.

KU KARANTA: Gwamnati ta ba yan sanda umurnin damke Rochas Okorocha

Hussaina ya kara da cewa kamfaninsa ta dukufa wajen taimakawa gwamnoni jihohi daban-daban wajen inganta kiwon lafiya a jihohinsu domin jin dadin al'ummmarsu.

Ya roki gwamnatin jihar su yi amfani da wadannan kayayyaki yadda ya kamata domin amfanin al'umma.

Sakataren din-din-din na ma'aikatar lafiyar jihar, Dakta Yahaya Yarima, ya ce wannan kyauta zai taimaka wajen dakile matsalar rashin kayayyaki a asibitocin jihar.

Ya yi kira da masu hannu da shuni da kungoyoyi sun taimaka wajen inganta kiwon lafiya ga yan Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel