Shugaba Buhari ya yi wa Aliko Dangote ta’aziyya akan babban rashi na yan uwansa 3 da yayi

Shugaba Buhari ya yi wa Aliko Dangote ta’aziyya akan babban rashi na yan uwansa 3 da yayi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 26 ga watan Agusta, ya yi ta’aziyya ga Alhaji Aliko Dangote, mai kudin Afrika kuma shahararren da kasuwa, akan rashin wasu ahlinsa da yayi.

Ahlin mai girma sun rasa mutane uku, dan uwan Aliko, Madugu Dantata; kawunsa, Alhaji Murtala Dantata da Alhaji Sa’idu Fanta, wani dan danginsu.

A wani sakon jaje zuwa ga Aliko Dangote, da ahlin Dantata da kuma gwamnati da mutanen jihar Kano ta hannun Boss Mustapha, babban sakataren gwamnatin tarayya, Shugaba Buhari ya bayyana rashin, wanda ya afku a kai-a kai a matsayin babban rashi sannan cewa ya zama dole a karbe shi a matsayin nufin Allah.

Ya roki Allah da ya ji kan wadanda suka rasu sannan ya ba iyalansu karfin jure rashin da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: NYSC ba za ta biya kudin fansar yan bautar kasar da aka yi garkuwa da su ba – DG

A wani labarin, mun ji cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya nada Mista Ahmad Rufai Zakari, da wurin tsohuwar hukumar zabe (INEC) ta rikon kwarya, Amina Zakari, a matsayin mai bashi shawara a kan aiyukan cigaban kasa.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Ahmad Zakari ya mika sakon godiya ga shugaba Buhari a kan mukamin da ya bashi tare da bayyana cewa zai yi iya bakin kokarinsa wajen bawa gwamnatin Buhari gudunmawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel