Jirgin sama ke sauke wa ubangidana makamai a cikin jeji – Dan fashi

Jirgin sama ke sauke wa ubangidana makamai a cikin jeji – Dan fashi

Wani dan fashi mai shekara 20 da aka ambata da suna Aliu Musa, ya bayyana a ranar Laraba, 20 ga watan Agusta, cewa sau daya ya taba ganin jirgin sama tana sauke ma maigidansa makamai a jejin Dinya a Karamar Hukumar Kankara dake jihar Katsina.

Musa, tare da abokin aikinsa, Samanu Isa dan shekara 18, sun kasance daga cikin yan fashin da hedikwatar rundunar yan sandan jihar Katsina ta gurfanar.

Musa ya fada ma yan jarida cewa an sauke ma maigidansa makaman ne da rana tsaka a cikin jejin.

Yayin da yake cigaba da magana, Musa yace ya kashe akalla mutane biyar a lokuta daban-daban na gudanar da ayyukansu, ya kara da cewa ana biyan shi naira 17,000 a kowani aiki.

Yace har ila yau ba a samu kama shugaban kungiyar shi ba.

Kakakin yan sandan jihar, ASP Anas Gezawa wanda yayi jawabi ga manema labarai a madadin kwamishinan yan sanda, Sanusi Buba kafin gurfanar da masu laifin, yace kungiyar da Musa da Isah ke ciki ta kashe akalla mutane 25 a aikin fashi daban-daban.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin tarayya ta zuba N600bn cikin kasuwar wutar lantarki

Gezawa yace, “a ranar 15 ga watan Agusta, 2019 rundunar yan sandan ta kama Salmanu Isah dan shekara 18 dan kauyen Danbago a karamar hukumar Kankara; da Aliyu Musa dan shekara 20 dan kauyen Chediya har ila yau dan Karamar Hukumar Kankara.

Kakakin yan sandan yace ana samun nasara a binciken da ake gudanarwa akan lamarin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel