Yanzu Yanzu: Hanyar Lagas-Abeokuta ya tushe yayinda Yarbawa da Hausawa yan kasuwa ke rikici

Yanzu Yanzu: Hanyar Lagas-Abeokuta ya tushe yayinda Yarbawa da Hausawa yan kasuwa ke rikici

Wani rikici ya barke tsakanin Yarbawa da Hausawa yan kasuwa a kasuwar Oke-Odo da ke hanyar babban tiin Lagas Abeokua wanda yayi sanadiyar tushewar hanya a yankin.

Ababen hawa da suka doshi hanyar Lagas daga Sando a jihar Ogun da wadanda ke afiya zuwa Abule-Egba daga Oshodi da sauran yankunan jihar sun tsaya chak.

Wani mazaunin yankin ya fada ma jaridar TheCable cewa rikicin ya fara ne a daren jiya lokacin da yan kasuwa a kasuwar kayan abinci suka fara rigima kan wani lamari da ba a sani ba.

An tattaro cewa lamarin ya munana a safiyar ranar Lahadi lokacin da yan kasuwa suka fara kone-kone.

Yanzu Yanzu: Hanyar Lagas-Abeokuta ya tushe yayinda Yarbawa da Hausawa yan kasuwa ke rikici
Yanzu Yanzu: Hanyar Lagas-Abeokuta ya tushe yayinda Yarbawa da Hausawa yan kasuwa ke rikici
Asali: Facebook

A halin da ake ciki, mun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya a ranar Lahadi, 18 ga watan Agusta, ta yi nasarar takaita rikicin da ya fara a tsakanin Hausa da Yarbawa a wani yanki na jihar Lagas.

Yanzu Yanzu: Hanyar Lagas-Abeokuta ya tushe yayinda Yarbawa da Hausawa yan kasuwa ke rikici
Yanzu Yanzu: Hanyar Lagas-Abeokuta ya tushe yayinda Yarbawa da Hausawa yan kasuwa ke rikici
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Wata baturiya da mahaifinta sun kashe likitan Najeriya ta hanyar caccaka masa wuka

Ba a san dalilin barkewar rikicin ba, amma rundunar RRS a wani jawabi da ta saki, tace jami’anta na a kasa domin daidaita lamarin da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel