Tsaro: Matawalle ya yiwa Buhari jawabin cigaban da aka samu a bangaren tsaron Zamfara

Tsaro: Matawalle ya yiwa Buhari jawabin cigaban da aka samu a bangaren tsaron Zamfara

-Gwamna Bello Matawalle ya kaiwa Shugaba Buhari ziyara a gidansa na Daura

-Matawalle a lokacin ziyarar ya yiwa shugaban kasa bayani game da nasarorin da ya samu a bangaren tsaron Jihar Zamfara

-Ganduje ya kai wa Shugaban kasan ziyara domin taya shi murnar bikin babbar sallah

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle a jiya Alhamis ya yiwa Shugaba Buhari jawabi a kan nasarar da ya samu wurin kawo karshen rikicin ‘yan bindiga a Zamfara.

Gwamnan ya gana da Shugaban kasan ne a gidansa dake Daura, inda kuma bayan sun kammala ganawar ya zanta da manema labarai a kan abinda suka tattauna.

KU KARANTA:Abinda ya kamata ku sani game da Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha

“ Na yiwa Shugaban kasan jawabi a kan nasarar da muka samu daga lokacin da muka hau mulki zuwa yanzu. Kamar da yadda kuka sani a cikin watanni biyu kacal kuma ina mai baku tabbacin cewa aiki yanzu ma muka fara.” Inji gwamnan.

Ya kara da cewa a yanzu akwai kwanciyar hankali da zaman lafiya a Zamfara, wannan kuma wani abu ne da shekarun baya Jihar Zamfara ta rasa.

“ A yanzu al’ummar hausawa da Fulani na zama tare lami lafiya. A kullum bamu da aiki sai kira ga jama’armu a kan sanin muhimmancin zaman lafiya da junansu.

“ Mun samu sulhunta ‘yan bindigan da sauran al’ummomin da rikicin ya shafa ba tare da basu kudi ko wani abin ba. Hakan ya sa duk wadanda aka kama yanzu an sako sub a tare da biyan fansar ko kwabo ba.” A cewar Matawalle.

Har wa yau, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya ziyarci Daura domin yiwa Shugaban kasa barka da sallah a ranar Alhamis.

Ganduje ya yiwa Shugaba Buhari tare da yi masa bayanin yadda ziyarar Shugaban Guinea zuwa Jihar Kano ta kasance.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel