Idan kazo Daura kadai muke samun wuta, hakiman yankin Daura sun shaidawa Buhari

Idan kazo Daura kadai muke samun wuta, hakiman yankin Daura sun shaidawa Buhari

-Hakiman yankin Daura sun ziyarci Buhari domin taya shi murnar bikin sallah

-Daya daga cikin hakimin ya kokawa Shugaban kasan cewa idan baya gari wutar lantarki ba ta zama a yankin nasu

-Yusuf Bello Mai-aduwa ya yabawa Buhari bisa rattaba hannu kan kudurin ginin kwalejin fasaha da kere-kere a Daura

Hakiman kananan hukumomi biyar dake karkashin masarautar Daura a jiya Talata sun shaidawa Shugaba Muhammadu Buhari cewa idan ya dawo ne kawai suke samun wutar lantarki a ko wane yini.

Shugaban kasan ya karbi bakuncin hakiman daga kananan hukumomi biyar inda suka ziyarce shi domin taya shi murnar sallah babba.

KU KARANTA:Kisan ‘yan sanda: Ku rika yin tafiya cikin farin kaya, shawarar Buratai ga sojoji

Daya daga cikin hakiman, Muhammad Saleh ya ce: “ A duk lokacin da shugaban kasan ke gari muna samun wutar lantarki tsawon awa 24. Amma idan bai gari wutar tamu ko zama ba tayi.”

Bugu da kari, ya jinjinawa shugaban kasan a kan rattaba hannun da yayi bisa kudurin gina kwalejin fasaha da kere-kere mallakar gwamnatin tarayya a Daura, bayan al’ummar yankin tayi korafi a kan wannan bukatar.

Har ila yau, wani hakimin na daban, Yusuf Bello Mai-aduwa ya godewa ‘yan Najeriya a dalilin sake zabar shugaban kasa a karo na biyu domin ya ja akalar kasar nan tsawon wasu shekara hudu, inda yake cewa ba zai ba Najeriya kunya ba.

Ana ta jawabin kuwa, Hajiya Talatu Nasir, babbar sakatare a ma’aikatar yada labarai ta kasa ta ce, gwamnatin Shugaba Buhari ta tallafawa mata da yawa ta yadda wasu daga cikinsu ke kiwon kaji da kuma dabbobi domin dogaro ga kai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel