Jiragen sojoji sun yiwa ‘yan Boko Haram barin wuta a Jejin Sambisa

Jiragen sojoji sun yiwa ‘yan Boko Haram barin wuta a Jejin Sambisa

-Mayakan boko haram sun sha kashi a hannu rundunar sojin saman Najeriya ta NAF

-Kakakin rundunar sojin saman Najeriya Ibikunle Daramola ne ya tabbatar mana da aukuwar wannan lamari inda ya ce jiragen yaki biyu ne kacal suka kai harin

-A cikin zancen kakakin ya bayyana mana cewa an kashe mutane da yawa wadanda suke 'yan kungiyar boko haram a sakamakon wannan hari

Jirage biyu na rundunar sojojin sama ta Najeriya wato NAF sun kona wata mabuyar ‘yan Boko Haram dake shiyyar Alafa cikin Jejin Sambisa na jihar Borno inda suka kashe da dama cikinsu.

An kai wannan harin jirgin saman ne ranar Alhamis, bayan da aka samu wadansu bayanan sirri da suka tabbatar lallai mayakan na Boko Haram suna nan a wurin tare da makamansu.

KU KARANTA:Satar N400m: Rundunar Soji ta kama iyalan daya daga cikin sojojin da suka tsere

Kakakin rundunar sojin saman, Ibikunle Daramola ya fitar da wani bayani a ranar Juma’a inda yake cewa, sashen kai harin jiragen sama na Operation Lafiya Dole ne ya tura jirage biyu zuwa ainihin wurin.

Daramola ya ce: “ A cigaba da yakar kungiyar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, sashen yaki da jiragen sama na Operation Lafiya Dole ya ragargaza mabuyar ‘yan boko haram dake Alafa a cikin Jejin Sambisa na Borno.

“ A sakamakon wannan harin, jami’anmu sunyi nasarar kashe yan ta’addan da dama. Jiragen biyu da suka isa wurin da ‘yan ta’addan suke sun dau seti mai kyau wanda ya ba su damar kashe da yawa daga cikinsu da kuma wargaza mabuyar baki dayanta.”

A wani labarin kuwa, za kuji cewa, rundunar sojin Najeriya ta tsare mata da yara uku na daya daga cikin sojojin da suka tafka satar kudi naira miliyan 400.

Matar mai suna Ayo Oluwaniyi tare da diyanta uku ita ce matar Kofur Gabriel Oluwaniyi wanda yake daya daga cikin sojoji biyar din da suka tsere da N400m wanda aka aike su kaiwa Kaduna daga Sokoto.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel