Dattawa da matasan jam'iyar APC a jihar Bauchi na goyon bayan baiwa tsohon gwamnan jihar minista
-Dattawa da matasa magoya bayan APC a Bauchi sun bayyana goyon bayansu kan ayi wa tsohon gwamnan jihar minista
-Kungiyoyin biyu sun yi kira ga Shugaba Buhari cewa kada ya saurari jam'iyyar adawa ta PDP ta duk wani mai kushe a kan lamarin
Kungiyar dattawan jam’iyyar APC dake kudancin Bauchi ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari kan cewa ya yi watsi da kiran ‘yan PDP na cewa ya manta da maganar ba wa tsohon gwamnan Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar muqamin minista.
Da yake bayani ga manema labarai ranar Alhamis a Bauchi, shugaban kungiyar, Alhaji Bamanga Muhammad ya roki Shugaba Buhari da ya duba mutane irinsu Gwamna Abubakar wadanda suka yi mashi hidima a zaben da ya gabata.
KU KARANTA:Kasuwancin kasa da kasa: Lawan ya gana da Jakadan kasar China a Abuja
Dattawan sun ce, ya kamata a bai wa tsohon gwamnan damar yiwa kasa hidima ta hanyar ba shi wani mukami, musamman saboda rawar ganin da ya taka cikin nasarar Shugaban kasa a zaben 2019.
“ Duk wani gutsuri tsoma da kushe da za’a kawo a kansa magana ce maras tasiri. Sanin kowa ne Abubakar shi ne jagoran APC a jihar Bauchi kuma shi ne mafi dacewa na ya wakilci jihar a matakin minista. Mu a matsayinmu na dattawan jihar Bauchi ba za mu bari a shafa masa kashin kaji ba.” A cewar dattawan.
Har ila yau, Majalisar matasan APC na jihar Bauchi sun yi irin wannan kiran ga Shugaba Muhammadu Buhari. Inda suka nemi a sanya sunan tsohon gwamnan cikin jerin wadanda za a bai wa muqamin minista.
Sakatare janar na majalisar, Kwamaret Nasiru Nuhu Cigari shi ne yayi wannan kira, inda yake cewa, yakamata Shugaban kasa yayi kunnen uwar shegu da masu cewa kada a dauki Abubakar Muhammad a matsayin minista daga Bauchi saboda shi ne mafi dacewa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng