Assha: Wata budurwa ta kashe kanta bayan sun rabu da saurayinta

Assha: Wata budurwa ta kashe kanta bayan sun rabu da saurayinta

- Wata dalibar jami’ar Benin (UNIBEN), Christabel ta kashe kanta bayan sun rabu da masoyinta

- Christabel taa hallaka kanta ne ta hanyar shan maganin kwari

- Ta kuma bar wasika inda ta ambaci sunayen wasu mutane biyu a ciki

Wata dalibar jami’ar Benin (UNIBEN), Christabel ta kashe kanta a dakin kwananta dake unguwar Newton, Ekosodin a garin Benin bayan ta sha guba.

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa, marigayiyar ta sha maganin kashe kwari bayan ta hada shi da lemun kwalba, ta kuma bar wasika inda ta bayyana cewa zata kashe kanta saboda saurayinta ya rabu da ita.

Amman wata majiya ta kawo cewa an gano ledan sabulun wanki a inda aka tsinci gawarta.

Haka zalika, a wani rubutu a shafin zumunta daga wata ma’aikaciyar UNIBEN, an rahoto cewa wasikar, wanda a halin yanzu ya ke a hannun yan sanda a ofishin yan sanda a Ugbowo, an rubuta ta ne zuwa ga mutane biyu, sannan kuma an gayyace su zuwa ofishin yan sandan don amsa tambayoyi.

Rubutun yayi ikirarin cewa ba wait a kashe kanta saboda matsalar da ta samu da masoyinta bane kawai illa wasu al’amuran da ta kasa magancewa a tsakaninta da wadannan mutane biyun da ta ambata a wasikar.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta haramta siyar da man fetur cikin jarkoki a Adamawa, Borno da Yobe

“Wasikar bai bayyana abunda ya faru ba tsakaninta da mutane biyun da ta ambata, wannan dalilin ne yasa yan sanda suka gayyace su domin su bayyana dalilin da yasa marigayiyar kashe kanta,” cewar rubutun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel