Sakamakon zaben June 12 na kowacce jiha da dalilin da yasa IBB yayi watsi dashi

Sakamakon zaben June 12 na kowacce jiha da dalilin da yasa IBB yayi watsi dashi

Kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito mun samo muku sakamakon zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Yuni da aka yi a shekarar 1993, tsakanin jam'iyyar SDP da NRC

Sakamakon zaben ranar 12 ga watan Yuni, shekarar 1993, da aka yi watsi dashi, wanda hukumar zabe ta lokacin ta bai wa wata kotu a jihar Legas. Kamar yadda sakamakon zaben ya nuna Cif MKO Abiola ya samu kuri'u 8,341,309 a karkashin jam'iyyar SDP, hakan ya bashi damar kada abokin hamayyarsa Bashir Tofa wanda ya samu kuri'u 5,952,807 a karkashin jam'iyyar NRC.

Duba sakamakon zaben na kowacce jiha dake kasar nan a lokacin:

Abia

SDP - 105,273

NRC - 151,227

Adamawa

SDP - 140,875

NRC - 167,239

Akwa Ibom

SDP - 214,787

NRC - 199,342

Anambra

SDP - 212,024

NRC - 159,258

Bauchi

SDP - 339,339

NRC - 524,836

Benue

SDP - 246,830

NRC - 186,302

Borno

SDP - 153,496

NRC - 128,684

Cross River

SDP - 189,303

NRC - 153,452

Delta

SDP - 327,277

NRC - 145,001

Edo

SDP - 205,407

NRC - 103,572

Enugu

SDP - 263,101

NRC - 284,050

Imo

SDP - 159,350

NRC - 195,836

Jigawa

SDP - 138,552

NRC - 89,836

Kaduna

SDP - 389,713

NRC - 356,860

Kano

SDP - 169,619

NRC - 154,809

Katsina

SDP - 171,162

NRC - 271,077

Kebbi

SDP - 70,219

NRC - 144,808

Kogi

SDP - 222,760

NRC - 265,732

Kwara

SDP - 272,270

NRC - 80,209

Lagos

SDP - 883,965

NRC - 149,432

Niger

SDP - 136,350

NRC - 221,437

Ogun

SDP - 425,725

NRC - 59,246

Ondo

SDP - 883,024

NRC - 162,994

Osun

SDP - 365,266

NRC - 72,068

Oyo

SDP - 536,011

NRC - 105,788

Plateau

SDP - 417,565

NRC - 259,394

Rivers

SDP - 370,578

NRC - 640,973

Sokoto

SDP - 97,887

NRC - 372,250

Taraba

SDP - 101,887

NRC - 64,001

Yobe

SDP - 111,887

NRC - 64,061

FCT Abuja

SDP - 19,968

NRC - 18,313

Jimilla

SDP - 8,341,309

NRC - 5,952,087

KU KARANTA: Murtala: Ya sanar da kotu cewa wallahi ba zai saki matarsa ba har sai ta biyashi sadakin naira miliyan 3.5 din shi

A bayanin da tsohon shugaban kasar mulkin soja na wancan lokacin yayi, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, yayi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yuni, shekarar 1993.

Duk da dai tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa an gabatar da zaben cikin kwanciyar hankali, amma duk da haka yayi watsi da sakamakon zaben.

"Mun yarda cewa anyi zabe an kammala lami lafiya. Amma akwai wuraren da muke zargin an gabatar da magudin zabe. An kashe kimanin naira biliyan 2.1 wurin gabatar da zaben. Mun samu shaidu da suke nuna cewa wasu malaman zabe sun gabatar da magudin zabe, inda aka yaudaresu da kudi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel