Buratai ya kaddamar da gidajen ma'aikata 20 a Jami'ar Sojoji da ke Biu

Buratai ya kaddamar da gidajen ma'aikata 20 a Jami'ar Sojoji da ke Biu

A ranar Talata 21 ga watan Mayu ne shugaban hafsin hafsohin Najeriya, Lafanat Janar Tukur Buratai ya kaddamar da sabbin gidajen ma'aikatan Jami'ar Sojojin Najeriya da ke Biu, NAUB a Jihar Borno.

A jawabin da ya yi wurin taron, Mr Buratai ya ce an kawatta gidajen masu dakuna uku da kayan daki da na'urorin sanyaya daki.

"Wannan sune rukunin gidaje na farko da ake ginawa domin ma'aikatan jami'ar.

"Wannan itace jami'a mafi kankantan shekaru a kasar nan kamar yadda kuka sani, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da jami'ar a ranar 30 ga watan Oktoban 2018 inda ya samu wakilcin Ministan Ilimi.

Buratai ya kaddamar da gidajen ma'aikata 20 a Jami'ar Sojoji da ke Biu

Buratai ya kaddamar da gidajen ma'aikata 20 a Jami'ar Sojoji da ke Biu
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Rudani: Kwamandan soji ya kaiwa tawagar mataimakin gwamna hari a Maiduguri

"Amma a yau, mun cimma wata nasara inda muka gida gidajen ma'aikata guda 20," inji shi.

A cewarsa, har yanzu akwai wasu ayyukan da ake gudanarwa da za a kammala cikin watanni uku masu zuwa.

Ya yabawa kokarin mutane masu zaman kansu, kamfanoni da hukumomin gwamnati da suka bayar da gudunmawa wurin cigabar jami'ar.

Mr Buratai ya ce daliban jami'ar na farko suna gab da kammala zagon karatunsu na farko.

A jawabinsa, shugaban jami'ar, Farfesa David Malgwi ya mika godiyarsa da Mr Buratai bisa gudunmawar da ya bayar wurin ganin jami'ar tana cigaba.

Ya yaba masa saboda yadda ya jajirce wurin ganin an kawatta gidajen da kayayaki masu inganci da nagarta domin jin dadin ma'aikatan jami'ar.

Mr Malgwi ya bukaci wadanda za su amfana da gidajen su kula da gidajen domin tabbatar da cewa sunyi karko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel