Zamfara: Masu garkuwa sun karbi kudin fansa N2.5m sannan suka sace dan mutumin da suka yi garkuwa dashi

Zamfara: Masu garkuwa sun karbi kudin fansa N2.5m sannan suka sace dan mutumin da suka yi garkuwa dashi

Masu garkuwa da mutane sun tilasta wani dan shekara goma sha takwas mai suna Abubakar Sani daga kauyen Birnin Magaji dake jihar Zamfara mika kudin fansar mahaifinsa kimanin naira miliyan 2.5.

Wata majiya daga iyalan mutumin tace har ila yau dai, masu garkuwan sun kuma yin gaba da dan mutumin ma.

Sanusi Sani, yaya ga Abubakar Sanusi, ya fada ma jaridar Premium Times a ranar Juma’a cewa anyi yarjejeniya akan kudin fansar ta wayar talho da yan bindigan.

Yace yan bindigan sun yi garkuwa da Abubakar bayan sun karbi kudin fansan sannan duk da haka sun tafi da mashin din shi.

Zamfara: Masu garkuwa sun karbi kudin fansa N2.5m sannan suka sace dan mutumin da suka yi garkuwa dashi
Zamfara: Masu garkuwa sun karbi kudin fansa N2.5m sannan suka sace dan mutumin da suka yi garkuwa dashi
Asali: Depositphotos

Sanusi yace yan bindigan sun nemi karin kudin fansa. Yace yan bindigan sun yi kira suka kuma tabbatar da cewa mai rike da kudin fansan ne suka kama.

Garkuwa da al’umma ya zama ruwan dare a jihar Zamfara duk da tarin jami’an tsaro da aka tura da kuma biliyoyin nairori da aka saki don inganta lamarin tsaro.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yakubu Gowon ya yanke jiki ya fadi a wajen jana’iza a Delta

Yan bindiga suna kai hare hare da kuma garkuwa da manoma a duk lokacin da suka ga dama.

Lokacin damina ya zo amman yawancin manoma a yankunan da aka fi sani da nona baza su yi noma ba wannan karon saboda tsoron kada ayi garkuwa da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel