Babu wanda zai iya tilastawa yan Najeriya yin wani addini, inji wani malamin musulunci

Babu wanda zai iya tilastawa yan Najeriya yin wani addini, inji wani malamin musulunci

-Kowane dan Najeriya na da 'yancin yin addinin da yaga dama saboda dokar kasa bata hana yin hakan ba

-Babu wanda ke da karfin sa 'yan Najeriya yin ko wane addinin da basu ga dama ba

Babban limamin masallacin yarbawa dake Umuagu Asaba mai suna Alhaji Adam Ayokunnu ya jaddada cewa babu wanda zai iya tilasta addnini ga ‘yan Najeriya ko da kuwa shugaba Buharine.

Da yake zantawa da jaridar INDEPENDENT a garin Asaba malamin yace Najeriya tafi karfin a kafa mata irin wannan doka. Yayi kira ga jama’a da suyi watsi da batun da wasu ke fadi na cewa akwai yinkurin musuluntar da Najeriya, wannan ba komi bane face adawa da jita-jita daga wurin magauta duk ta dalilin siyasa.

Babu wanda zai iya tilastawa yan Najeriya yin wani addini, inji wani malamin musulunci

Babu wanda zai iya tilastawa yan Najeriya yin wani addini, inji wani malamin musulunci
Source: UGC

KU KARANTA:Tinubu ba zai mulki Najeriya ba, inji shugaban Miyetti Allah

Ya kara da cewa sam ba laifi bane ya kasance akwai addinai iri-iri, saboda Allah ma Yayi hallita ne cikin kabilu, addinai da kuma jinsi daban-daban.

A cewarsa: “ Wannan maganar ba gaskiya bace. Mutum daya ba zai iya musuluntar da Najeriya ba, yau ko da dan daka haifane ya ga dama yace shi ba zai yi addininka ba, idan haka ta faru tursasashi zakayi?

“ A irin yawan da muke dashi na sama da mutane miliyan 160 sam ba zai yiwu ba ace an maida kowa ya zama musulmi. Dalili kuwa anan shine gwamnati tana bin tsarin dokokin mulkin Najeriya ne wanda kuma akwai ‘yanci yin addinin da mutum yaga dama.” Inji malamin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel