Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 40, sun ceto mutane a Jihar katsina

Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 40, sun ceto mutane a Jihar katsina

- Atisayen Puff Ader ya fara haifan 'da mai ido

- Bayan kawar da masu garkuwa da mutane a jihar Kaduna, an samu nasara a jihar Katsina

Sabon atisaye da sifeton yan sanda, Mohammed Abubakar kaddamar wato “puff adder,” domin ganin cewa an kawar da matsalar yan bindiga da masu garkuwa da mutane ya fara haifan 'da mai ido yayinda yan sanda a jihar katsina sun kama yan ta’adda 40 wa’inda sun kunshi masu garkuwa da mutane, Yan bindiga, Yan fashi da makami,da kuma masu asiri.

Kwamishinan yan sanda na Jihar, Sanusi Buba yayinda yake bayyana yan ta’addan da wa’inda aka ceto ga manema labarai a hedkwatar yan sandar, ya bayyana cewa an samu wannan nasarar ne a sakamakon binciken leken asiri, bunkasar sintiri, samun cinne daga al’umman gari da sauran hukumomi ta hanyar atisayen Puff adder.

Ya kara da cewa “Da taimakon Allah da kuma taimakon sauran jami’ai ina farin cikin bayyana nasarar da aka samu daga hukumomin yan sanda na wannan jihar.”

Wasu daga cikin wa’inda aka kama tare da bindigar AK-47 da wasu makamai suna masu garkuwa da mutanen da suka addabi karamar hukumar Safana da Basari.

An kamasu ne a yayinda da sukayi garkuwa da Hajia Habiba mai kimanin shekara 65 yar kauyen Yar-Liyau a kamar hukumar Kurfi, inda suka bukaci kudi kimanin miliyan 15 matsayin fansa.

KU KARANTA: Mutum takwas ne suka mutu, yayinda 148 suka samu rauni cikin watanni uku, inji Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC)

Bisa ga bayanin kwamishinan Yan sandan, ya nuna sauran abinda aka anso daga gangamin sun hada da babur, adda guda biyu, da kudi kimanin N218,000.

Kwamishinan ya bayyana masu kaima yan garkuwan kayayyaki kamar man fetir, Babura da kuma gyaran makamansu.

An kama wani Alhaji Sale Musa, mai kimanin shekara 55, dan kauyen Wagini dake karamar hukumar Batsari da galolin man fetir cike da wata mota yana kokarin tsallake dajin Rugu.

Yayi ikirarin cewa yana samo man fetir dinne daga wani manajan daya daga cikin gidan man dake karamar hukumar Batagarawa.

Kwamishinan ya dau alkawarin cewa zai cigaba da sanar da manema labarai atisayen dake wakana a kananan hukumomin, Yace ana cigaba da bincike akan wa’inda aka kama kuma da zaran an kammala za’a shigar da su kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel