Shugabancin majalisa: Wamakko ya karyata fadin cewa sanatoci 82 na goyon bayan Ahmed Lawan

Shugabancin majalisa: Wamakko ya karyata fadin cewa sanatoci 82 na goyon bayan Ahmed Lawan

- Aliyu Wamakko ya karyata rahotannin da ke cewa shi yace sanatoci 82 na goyon bayan takarar Sanata Ahmed Lawan na son zama Shugaban majalisar dattawa

- An kawo cewa Wamakko wanda ke wakiltan Sokoto ta arewa yace sanatoci 82 na bayan Ahmed Lwan

- A cewar jawabin an alakanta Wamakko da lamarin bisa kuskure ne

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Shugaban kungiyar sanatocin arewa ya karyata rahotannin da ke cewa shi yace sanatoci 82 na goyon bayan takarar Sanata Ahmed Lawan na son zama Shugaban majalisar dattawa.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da aka saki a Sokoto daga hannun mai ba Wamakko shawara a kafofin watsa labarai, Bashir Mani.

Shugabancin majalisa: Wamakko ya karyata fadin cewa sanatoci 82 na goyon bayan Ahmed Lawan
Shugabancin majalisa: Wamakko ya karyata fadin cewa sanatoci 82 na goyon bayan Ahmed Lawan
Asali: Depositphotos

A cewar jawabin, an alakanta hakan ne da Sanata Wamakko, wanda ke wakiltan Sokoto ta arewa bisa kuskure.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Kakakin majalisar dattawa, Sanata Abdullahi Sabi ya nuna tabbacin cewa takwaransa, Ahmad Lawan, zai lashe kuri’un kaso biyu cikin uku don zama Shugaban majalisar dattawan.

KU KARANTA KUMA: Lawan zai samu kuri’u 2/3 don zama Shugaban majalisar dattawa – Kakakin majalisar dattawa

Sabi, wanda ya bayar da tabbacin yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu a Abuja, yace da amincewar jam’ iyyar All Progressives Congress’ (APC) da kuma tabbacin da yake samu daga zababbun sanatoci a fadin jam’iyyar, Lawan zai yi nasarar lashe kujerar, kamfanin dillanin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito.

Sanata Sabi (APC-Niger), wanda ya sakie lashe zabe a majalisar dattawa ta 9, yace tuni an fara tattaunawa don marawa Lawan baya wajen ganin ya zama Shugaban majalisar dattawan.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel